Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kogi Ya Fice Daga PDP Zuwa APC a Abuja

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kogi Ya Fice Daga PDP Zuwa APC a Abuja

  • Yayin da ake tunkarar zaben gwamnan jihar Kogi, jam'iyyar APC ta yi babban kamu daga babbar jam'iyyar adawa PDP
  • Tsohon mataimakin gwamnan jihar, Arc Yomi Awoniyi, ya shiga jam'iyyar APC a hukumance ranar Talata a hedkwata da ke Abuja
  • Gwamna Yahaya Bello ya yaba wa Awoniyi, inda ya ce wannan alama ce ta mutane sun gamsu da gwamnatin APC

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kogi, Arc Yomi Awoniyi, ya tabbatar da koma wa jam'iyyar APC a hukumance gabanin zaɓen gwamnan jihar ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Awoniyi, wanda ya nuna gansuwarsa da gwamnatin Yahaya Bello, an karbe shi a hukumance zuwa inuwar APC a hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja, ranar Talata.

Tsohon gwamnan jihar Kogi tare da shugaban APC na ƙasa.
Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kogi Ya Fice Daga PDP Zuwa APC a Abuja Hoto: Dailytrust
Asali: UGC

Ya rike mukamin mataimakin gwamnan jihar Kogi daga 2011 zuwa 2015 a lokacin gwamnatin Captain Idris Wada, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Hadimai 2 Na Gwamnan PDP da Wasu Manyan Jiga-Jigai Sun Koma APC Ana Dab Da Sabon Zaɓe

Meyasa ya zaɓi shiga jam'iyyar APC?

Tsohon jigon jam'iyyar PDP ya aminta cewa siyasar Kogi tana da sarkakiya da kalubale, ya kuma yabawa Gwamna Yahaya Bello bisa yadda ya bai wa mara ɗa kunya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mista Awoniyi ya ce:

"Na yi aiki a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kogi tsakanin 2011 zuwa 2015. Na san jihar sosai, kuma zan iya gaya muku cewa gwamna mai ci yanzu ya yi fice sosai ta fuskar jagoranci da shugabanci nagari."
"Wadannan halaye da nagarta na daga cikin dalilan da suka ja hankalina na yanke shawarar shiga APC domin na goya masa baya da kuma gwamnati mai zuwa."

Gwamna Yahaya Bello ya yaba da matakin

Da yake maraba da Awoniya, gwamna Yahaya Bello wanda ya ayyana shi a matsayin "Babban kifi" ya ce matakin da ya ɗauka na shiga APC shi ne ya dace.

Kara karanta wannan

Al’ummar Yarbawa Sun Yi Wa Kwankwaso Da Gwamnatin Kano Addu’a Ta Musamman

Ya jaddada cewa matakin Awoniyi ya nuna karara yadda jama'a suka gamsu da nasarorin da ya samu da kuma yadda suke nuna goyon baya ga shugabancinsa domin ci gaban jihar.

A rahoton Tribune Online, Gwamnan ya ce:

"Ina mai farin cikin maraba da tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi, Arc Abayomi Awoniyi zuwa jam’iyyar mu a yau. Awoniyi fitaccen mutum ne da ya shigo tafiyar mu a APC."
"Na ji dadin matakin da ya ɗauka na shiga jam’iyyar mu, kuma ina mai tabbatar muku da cewa jam’iyyar APC za ta kara yi wa al’ummar jihar Kogi tulin ayyuka.”

Shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yaba wa tsohon mataimakin gwamna bisa sauya sheƙar da ya yi zuwa APC.

Yusuf Yusuf, wani jigon APC a Kano kuma ɗan amutun Ganduje, ya ce yana da yaƙinin APC zata ci gaba da samun nasara a zaɓuka domin shugaban kasa bai yi zaɓen tumun dare ba.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Bayyana Shirin APC Na Ƙara Kafa Gwamnati a Jihar Arewa Cikin Shekarar Nan 2023

Ɗan siyasan ya shaida wa wakilin Legit Hausa cewa Ganduje ɗan siyasa ne mai hangen nesa, kuma yana da jajircewa a duk abinda ya tasa a gaba.

"Abin da zan fara cewa Allah ya saka wa shugaban ƙasa da Alkairi, ai tunda ya ɗauko Ganduje ya ba shi kujera lamba ɗaya a jam'iyya mai mulki na san ba a yi zaɓen tumun dare ba."
"Yanzu mutane sun fara gani, zaɓen Kogi, Imo da Bayelsa ne ke tafe, da mu da su za mu ƙara tantance waye mai girma Ganduje a siyasar Najeriya. Wannan jawo mutanen da yake yi somin taɓi ne," in ji shi.

Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Gwale

A wani labarin, Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da Ciyaman ɗin karamar hukumar Gwale, Khalid Ishaq Diso, bisa zargin sayar da kadarorin gwamnati.

A halin yanzu majalisar ta kafa kwamitin wucin gadi da zai gudanar da bincike kana ta umarci mataimakin ciyaman ya maye gurbin na tsawon wata 3.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Ministan Tinubu Ya Tsoma Baki a Rigimar Jam'iyyar APC Da Korar Jiga-Jigai 84

Asali: Legit.ng

Online view pixel