Jerin Yan Majalisa Na Labour Party Da Aka Tsige Cikin Kwanaki 100 a Ofis Da Dalili

Jerin Yan Majalisa Na Labour Party Da Aka Tsige Cikin Kwanaki 100 a Ofis Da Dalili

Babban zaben 2023 da ya gabata ya yi silar samar da "jam'iyya mai karfi ta uku" a siyasar Najeriya, inda hakan ya kusa zama gagarumin barazana ga jam'iyyar APC mai mulki da kuma kokarin ture jam'iyyar PDP, daga matsayinta na babbar jam'iyyar adawa.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Masana harkokin siyasa da dama sun bayyana jam'iyyar Labour Party da dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi a matsayin "jam'iyya mai karfi", duba ga nasarar da suka samu a babban zaben da ya gabata.

Jiga-jigan jam'iyyar Labour Party
Jerin Yan Majalisa Na Labour Party Da Aka Tsige Cikin Kwanaki 100 a Ofis Da Dalili Hoto: Labour Party
Asali: Twitter

Dalilin da yasa ake yi wa Labour Party lakabi da jam'iyya mai karfi

Jam'iyyar Labour Party ta lashe wasu adadi na kujeru a majalisar dattaa da majalisar wakilai yayin da dan takararta na shugaban kasa, Obi, ya kayar da shugaban kasa Bola Tinubu a jihar Lagas inda ya fi karfi.

Kara karanta wannan

Hanzari ba gudu ba: Shehu Sani ya shawarci Wike kan yadda ya rabi APC, ya nemi ya bar PDP

Hakazalika, jam'iyyar Labour Party ta zama barazana ga PDP a kudu maso gabas, yankin da ake ganin a nan ne babbar jam'iyyar adawar ta fi karfi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gagarumin nasara yasa Labour Party ta zama jam'iyya mafi karfi ta uku. Sai dai kuma, cikin kanaki 100 da kafa sabuwar gwamnatin damokradiyya da ta fara aiki a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, kotun zabe ta tsige zababbun yan majalisa biyu.

An lissafo su a kasa:

Ngozi Okolie

An tsige Okolie a matsayin dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Aniocha/Oshimili a karkashi inuwar jam'iyyar Labour Party a ranar Litinin, 24 ga watan Yuli, kimanin watanni biyu bayan kafa majalisar dokokin kasa ta 10.

Kotun zaben majalisar tarayya a jihar Delta ta tsige Okelie kan hujjar cewa shi ba dan Labour Party bane lokacin da jam'iyyar ta zabe shi sannan ta ayyana Ndudi Elumelu, dan takarar PDP, wanda ya zo na biyu a zaben a matsayin wanda ya lashe zaben.

Kara karanta wannan

Da gaske ne sojin Nijar sun kori jakadun Najeriya, Amurka da Jamus a kasarsu? Ga gaskiyar batu

Seyi Sowunmi

Sowunmi shine mutum na biyu da kotun zaben majalisar dokoki ta tsige cikin kwanaki 100 a ofis a ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta.

Kotun zabe da ke zama a jihar Delta ta tsige dan majalisar mai akiltan mazabar Ojo a majalisar wakilai kan dalili iri daya da wanda yasa aka tsige Okolie.

Ganduje ya rantsar da sabbin mambobin NWC na APC

A wani labari na daban, mun ji cewa daga karshe jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta rantsar da sabbin mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) guda shida yayin da ake tsaka da gagarumin zanga-zanga.

An rantsar da su ne a sakatariyar jam'iyyar ta kasa da ke babban birnin tarayya Abuja a tsakar daren ranar Juma'a, 25 ga watan Agusta, saboda zanga-zangar da aka yi kan zaben sabbin mambobin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel