Nasara a Kotun Zabe: Kwankwaso, Abba Gida Gida Da Wasu Jiga-Jigan NNPP Sunyi Taron Addu’a Na Musamman a Kano

Nasara a Kotun Zabe: Kwankwaso, Abba Gida Gida Da Wasu Jiga-Jigan NNPP Sunyi Taron Addu’a Na Musamman a Kano

  • Gwamnatin jihar Kano ta sako Allah cikin lamarinta gabanin yanke hukunci a kan shari'ar da ake yi a kotun zaben gwamnan jihar Kano
  • Jagoran NNPP na kasa, Rabiu Kwankwaso, Gwamna Abba Gida Gida da wasu jiga-jigan jam'iyyar sun yi taron addu'a na musamman a Kano
  • Sun roki Allah ya basu nasara sannan ya hana masu kokarin sace kuri'un mutanen jihar ta kofar baya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta shirya wani taron addu'a na musamman don neman Allah ya hana masu shirin sace kuri'un al'ummar jihar Kano ta kofar baya samun nasara.

Taron addu'ar wanda aka gudanar a Filin Mahaha da ke hanyar BUK a ranar Asabar ya samu halartan babban jigon jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: An Kama Wanda Ake Zargi Da Hannu a Kashe Shugabar Alkalan Kotu a Arewacin Najeriya

Taron yan Kwankwasiyya
Kotun Zabe: Kwankwaso, Abba Gida-Gida Da Sauran Yan Kwankwasiyya Sun Yi addu’ar Neman Nasara Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Har ila yau, taron ya samu halartan gamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wato Aba Gida Gida da mataimakinsa, Kwamrad Aminu Abdussalam tare da sauran manyan masu ruwa da tsaki na gwamnatin jihar.

Dr. Sani Ashir ne ya jagoranci taron addu'an.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A jawabinsa, Ashir ya karanto cewa:

"Ya Allah, ga shugabanninmu, zababbun shugabanninmu, wadanda ka albarkace mu da su; shugabanninmu da muka zaba bisa jagorancinka. Don Allah ka kare su. Don Allah ya jagorance su zuwa hanya madaidaiciya.
“Ya Allah makiyan al’umma suna ta makirci da shirin bata shugabanninmu, Ya Allah! kayar da makiyan mutane.
"Ya Allah ka lalata makiyan jihar Kano a duk inda suke. Ya Allah, makiyan jihar na kokarin sace kuri'un mutane ta kofar baya. Ya Allah ka kulle masu kai sannan ka kayar da su.

Kara karanta wannan

Tsohon Hadimin Buhari Ya Yabawa Kokarin Gwamna Abba Gida Gida a Jihar Kano

"Ya Allah, Ka samar da zaman lafiya mai dorewa a jiharmu. Ya Allah ka albarkaci kasuwanni da makarantunmu. Ya Allak ka albarkaci kasuwanci da gonakinmu. Ya Allah ka albarkaci shugabanninmu sannan ka lalata makiyansu."

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kalubalantar nasarar Gwamna Yusuf a kotun zabe.

Kotun Zabe Ta Tanadi hukuncinta Kan Shari'ar Gwamnan Jihar Kano

Mun dai ji a baya cewa kotun sauraron shari'ar zaben gwamnan jihar Kano ta tanadi hukuncinta a kan ƙarar da ke ƙalubalantar nasarar Abba Gida-Gida.

Kotun zaben ta sanar da hakan ne a ranar Litinin, 21 ga watan Agustan 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel