Sanata Ya Tona Asirin Ƴan Siyasa, Ya Fadi Abin da Zai Faru Idan Ba Su Saci Dukiya Ba

Sanata Ya Tona Asirin Ƴan Siyasa, Ya Fadi Abin da Zai Faru Idan Ba Su Saci Dukiya Ba

  • Shugaban masu tsawatarwa a Majalisar Dattawa, Ali Ndume ya fadi dalilin da yasa yan siyasa ke satar kudi
  • Ndume ya ce ƴan siyasa na sata ne domin rabawa da yan mazabarsu wanda hakan ya zama musu dole saboda zabe
  • Sanatan ya kuma nuna goyon bayan kan hukuncin kisa ga wadanda suka saci kudi da ya kai N1trn a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Sanata Ali Ndume da ke wakiltar jihar Borno ta Kudu ya magantu kan halin ƴan siyasa na - bera.

Ndume ya bayyana cewa ƴan siyasa da dama na satar kudin al'umma ne domin su iya rabawa da talakawansu.

Kara karanta wannan

Atiku ya nemi takawa Bola Tinubu burki kan taba kudin ’yan fansho ayi ayyuka

Ndume ya tona asirin ƴan siyasa game da satar kudin al'umma
Sanata Ali Ndume ya bayyana abin da ke jawo ƴan siyasa satar kudin al'umma. Hoto: Sen. Ali Ndume.
Asali: Facebook

Sanata Ndume ya fadi musabbabin satar kudi

Sanatan ya bayyana haka ne a yayin hira da yan jaridu game da hukuncin kisa kan masu safarar kwayoyi, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ƴan siyasa za su rasa kujerunsu idan har ba su raba kudin da suka sata ba da ƴan mazabarsu, cewar rahoton Pulse.

"Idan ka kwatanta cin hanci na ƴan siyasa da na saura, namu ya sha bam-bam saboda mutane ne suke saka ƴan siyasa sata."
"Idan kayi sata, za ka zo ne ka raba da ƴan mazabarka, idan kuma ka ki yin haka to za ka rasa damar dawowa kujerarka karo na biyu, babu amfani yin sata kenan."
"Na dade a Majalisar Tarayya, ba zai yiwu ba na ki fadan gaskiya, idan za a yi hukuncin kisa ya kamata a hada da masu cin hanci."

Kara karanta wannan

"Yan siyasa na satar kudi ne domin su rabawa talakawa", Sanata Ndume ya fasa kwai

- Ali Ndume

Sanata Ndume ya goyi bayan hukuncin kisa

Ndume ya ce yana goyon bayan hukuncin kisa amma ba wai kawai mutum ya saci N1m ko N1bn ba, sai idan mutum ya saci N1trn zuwa sama.

Sanatan ya ce ƴan siyasar na satar ne domin rabawa da yan mazabarsu wanda hakan ba su cancanci hukunci mai tsanani ba.

Sanatoci sun kawo kudiri a Majalisa

A wani labarin, an ji cewa Majalisar Tarayya tana shirin amincewa da hukuncin kisa kan masu safarar kwayoyi a fadin Najeriya.

Majalisar ya dauki wannan mataki ne domin kawo sauyi a bangaren ayyukan hukumar NDLEA da kuma inganta lafiyar al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.