Gwamna Ya Maidawa Tsohon Kwamishinansa Martani, Ya Kira Shi ‘Dan Kwaya a Fili

Gwamna Ya Maidawa Tsohon Kwamishinansa Martani, Ya Kira Shi ‘Dan Kwaya a Fili

  • Siminalayi Fubara ya yi martani ga wanda ya ce Nyesom Wike ne ya taimake shi, da yanzu yana fama da aikin gwamnati
  • A wani bidiyo, Fubara ya caccaki tsohon kwamishinansa inda ya nuna ‘dan kwaya ne shi da bai san abin da yake fada ba
  • Gwamnan Ribas ya zargi wannan mutumi da ya ajiye mukaminsa da sakin baki alhali ya fita daga hayyacinsa saboda kwaya

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Rivers – Da alama Gwamna Siminalayi Fubara da gaske yake yi wajen yakar tsohon uban gidansa a siyasa watau Nyesom Wike.

Hakan ya kara fitowa fili a ‘yan kwanakin nan ganin yadda ake rikici tsakanin Siminalayi Fubara da wadanda ya ba mukami.

Kara karanta wannan

Rivers: Gwamna ya kuma ɗaga yatsa ga Wike, ya bugi kirji kan jikkata abokan gaba

Siminalayi Fubara
Mai girma Gwamna Siminalayi Fubara a Fatakwal Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Mai girma Gwamna Fubara ya yi caccaka

A wani bidiyo da AskPH People ya wallafa a dandalin X wanda ya fi shahara da Twitter, an ji gwamnan yana kalamai masu zafi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin Mai girma Siminalayi Fubara ya maidawa tsohon kwamishinansa na ayyuka martani kwanaki bayan ya yi murabus.

Hakan ya biyo bayan tsohon kwamishinan ya yi ikirarin Nyesom Wike ya taimakawa Fubara, da yanzu ma’aikacin gwamnati ne.

A cewar ‘dan siyasar, in ba domin alfarmar tsohon gwamnan ba, da yanzu Fubara yana mataki na 14 ko 15 a aikin gwamnati.

Raddin gwamna Simi Fubara ga kwamishina

Da alama wannan magana ba tayi wa gwamnan jihar Ribas dadi, Punch ta ce a ranar Laraba aka ji ya maida martani mai kaushi.

Gwamna Fubara yake cewa ya ji wani rikakken ‘dan kwaya yana magana, yake cewa idan mutum yana maye, babu abin da bai fada.

Kara karanta wannan

"Ko a jikina," Ministan Tinubu ya maida martani kan abubuwan da ke faruwa a Rivers

“Idan ba ka san mutane ba, sai ka rika magana da ganganci, kuma idan ka yi mankas, me kuma ake tunani?”
“Idan a 2010, ni ne Babban Akanta, mafi yawanku kun san aikin gwamnati, a ina zan kasance kafin shekarar 2022?”
“Idan ka yi magana saboda ka burge uban gidanka, sai ka yi magana da ganganci, amma ba zan biye wadannan maganganu ba.”

- Siminalayi Fubara

Gwamna yana binciken magajinsa

Sakamakon kalaman Uba Sani, yanzu ‘yan majalisar Kaduna suna binciken Nasir El-Rufai inda ana tunanin an samu sabanin siyasa.

Ana da labarin yadda Abba Gida Gida ya taso Abdullahi Ganduje gaba, kamar yadda Gwamnonin Sokoto, Benuwai da Osun su ka bi sahu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng