'Mutane 4 aka Sace ba 500 ba,' DHQ ta yi Bayani kan Satar Mutanen Zamfara

'Mutane 4 aka Sace ba 500 ba,' DHQ ta yi Bayani kan Satar Mutanen Zamfara

  • Hedikwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta karyata labarin cewa ‘yan ta’adda sun samu nasarar kutsawa karamar hukumar Zurmi tare da sace mutane 500
  • Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa mutane 4 aka dauke a harin, wanda ya saba da adadin wadanda ake yadawa
  • Tun bayan kai harin da bullar labarin ne shi ma Gwamnan Zamfara, Dauda Lawan Dare ya zargi wasu da ya kira makiya jihar da yada labaran karya kan harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara- Hedkwatar tsaron Najeriya ta musanta cewa mutane 500 yan bindiga su ka sace a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Siyasar 2027: Ka yi hankali da mutanen Arewa, Ibo sun fara gargadin Peter Obi

Rahotanni sun karade kafafen yada labarai cewa 'yan ta'adda sun sace mutane kimanin 500 a karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Gwamna Dauda Lawan
Hedikwatar tsaro ta musanta satar mutane 500 a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Twitter

Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba ya ce labarin kanzon kurege ake yadawa, kamar yadda Leadership News ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zamfara: "Mutane 4 aka sace," DHQ

Hedkwatar tsaron kasar nan ta bayyana cewa mutane hudu 'yan ta'adda su ka ce a karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara.

Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan, sabanin mutane 500 da aka ruwaito tun da farko.

Ya ce dakarun operation hadarin daji na iya bakin kokarinsu wajen dakile hare-haren 'yan bindigar.

Gwamnan Zamfara ya karyata labarin

Tun bayan bullar labarin sace mutane kimanin 500 ne gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya musanta labarin sace mutane 500 a wata karamar hukumar da ke jihar, kamar yadda TVC News ta wallafa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka 50, sun sace mutane sama da 500 a Arewa

An dai fara yada wani labarin sace mutane 500 a yankin karamar hukumar Birnin Magaji, abin da Gwamnan ya zargi wasu da ya bayyana da makiya jihar Zamfara da yada labaran karya kan harin.

Ana neman Halilu Buzu Ruwa a jallo

Mun kawo mu ku labarin cewa rundunar sojojin kasar nan ta bayyana neman wani Halilu Buzu ruwa a jallo bisa zargin aikata laifin ta’addanci.

Rundunar ta ce yanzu haka ta na aiki da sojojin Nijar domin kama dan ta’addan da ya gawurta wajen kai hare-hare wasu yankunan Arewacin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.