Al Mustapha Ya Tona Asirin Waɗanda Suka Lalata Tsaro a Najeriya, Ya Kawo Mafita

Al Mustapha Ya Tona Asirin Waɗanda Suka Lalata Tsaro a Najeriya, Ya Kawo Mafita

  • Tsohon dogarin marigayi Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya yi magana a kan matsalar tsaro da ta addabi Najeriya
  • Al-Mustapha ya ce babban matsalar da aka samu kan rashin tsaro a Najeriya laifin Shugabannin baya ne da suka gaza yin wani abu
  • Tsohon sojan ya koka kan yadda aka bar matsalar ta girma har zuwa yadda ba za a iya dakile ta da sauki ba, inda ya ce sai dai ayi amfani da kimiyya da dabaru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Manjo Hamza Al-Mustapha ya magantu kan yadda matsalar tsaro ya tabarbare a Najeriya.

Hamza Al-Mustapha ya ce matsalolin tsaro da ke fuskantar Najeriya laifin shugabannin da suka gabata ne.

Kara karanta wannan

Dan majalisar PDP ya nemi Tinubu ya fara tafiye tafiye a mota ko ya hau jirgin haya

Al-Mustapha ya bayyana wadanda suka lalata tsaron Najeriya
Manjo Hamza Al-Mustapha ya zargi shugabannin baya da lalata lamarin tsaro. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Hamza Al-Mustapha ya zargi shugabanni da sakaci

Tsohon dogarin Marigayi Sani Abacha ya ce wadanda ke da alhakin tsare jama'a da kawo zaman lafiya sun gaza yin katabus.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manjo Hamza Al-Mustapha ya bayyana haka yayin wani babban taron kasa da kasa da aka gudanar a birnin Abuja, cewar rahoton The Guardian.

Ya ce wannan matsala da ake ciki na rashin tsaro yana bukatar amfani da dabarun kimiyya domin dakile matsalar.

"Musabbabin rashin tsaro"- Al-Mustapha

Har ila yau, ya ce babban matsalar ita ce shugabannin da suka gabata sun gaza aiwatar da wani abu kan nauyin da aka daura musu yadda ya kamata.

Al-Mustapha ya ce rashin tsaron Najeriya da sauran ƙasashen Afrika an yi watsi da su tun da dadewa.

Tsohon sojan ya ce barin matsalar ya jawo kara dagula lamura a kasar wanda ya wuce gona da iri.

Kara karanta wannan

"Nigeria za ta murkushe 'yan ta'adda idan ta samu tallafi daga EU" Inji Ministan Tinubu

Al-Mustapha ya magantu kan tsadar fetur

A wani labarin, kun ji cewa Hamza Al-Mustapha ya yi wata magana da ta za ta iya zama hannunka mai sanda ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Dogarin tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya nuna sai an yi hattara da ‘yan kasuwa.

Al-Mustapha mai ritaya a wata hira da ya yi da ƴan jaridu ya ce masu harkar fetur za su iya rusa gwamnati gaba ɗaya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel