Shehu Sani Ya Shawarci Minista Wike Ya Bar PDP Ya Koma APC Saboda Wasu Dalilai Na Kare Mutuncin Kansa

Shehu Sani Ya Shawarci Minista Wike Ya Bar PDP Ya Koma APC Saboda Wasu Dalilai Na Kare Mutuncin Kansa

  • Tsohon dan majalisa kuma mai fafutukar kare hakkin bil’adama, Shehu Sani ya yi martani kan abin da Nyesom Wike ya yi a ‘yan kwanakin nan
  • Sani ya bukaci Wike da ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki biyo bayan samun shiga a tsagin shugaban kasa Bola Tinubu
  • Wike dai ya fake da kujerar minista a mulkin Tunibu duk da kasancewarsa dan PDP kuma ya yi gwamna na tsawon wa'adi a inuwar jam'iyyar

Jihar Kaduna – Tsohon dan majalisar dattawa Sanata Shehu Sani ya bayyana bukatar ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

A wata hira da jaridar Punch, Sani ya bukaci tsohon gwamnan jihar Ribas, Wike, da ya koma jam’iyyar APC mai mulki saboda ya samu damar yiwa jam’iyyar mai mulki hidima.

Kara karanta wannan

Yadda Ganduje Ya Dawo Cikin Lissafin Siyasa, Ya Wargaza Kawancen Kwankwaso-Tinubu

Hakazalika, ya ce barinsa PDP zai ba jam’iyyar damar tsayawa kekam a matsayin jam'iyyar adawa mai karfi a kasar.

Shehu Sani ya shawarci Wike ya bar PDP, ya koma APC
Shawarin Shu Sani ga Wike | Hotuna: @ShehuSani,Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tsohon dan majalisar, a cikin hirar da aka buga a ranar Lahadi, 27 ga watan Agusta, 2023, ya ce Wike zai fi mutunci idan ya koma APC kuma ya yi aiki ba tare da raba hankalinsa tsakanin jam’iyyu biyu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shawarin Shehu Sani ga Wike

Sani ya fada a tattaunawar ta sa da Punch cewa:

“Shawarata ita ce, Nyesom Wike ya koma APC kawai inda zai yi wa jam’iyyar hidima sannan kuma ya bar PDP ya taka rawarta na jam’iyyar adawa.
“Za a fi mutunci idan ya koma APC ya yi aiki ba tare da tsaiko daga bangarorin biyu ba, domin idan ya ci gaba da raba kafafunsa tsakanin APC da PDP, zai yi siyasarsa cikin rudani, rashin tsari da rashin kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Aiki ya fara: Daga zuwa, Ganduje ya yi sabbin nade-nade a kwamitin NWC na APC

"Abin da ya fi dacewa shi ne ya sauya sheka domin ya yi aiki tukuru ga Shugaba Tinubu da ma APC."

Dalilin da yasa aka ba Wike minista

A bangare guda, dalilin da yasa aka ba Nyesom Wike minista a karkashin mulkin Tinubu ya bayyana daga bakin sanata Adeseye Ogunlewe.

Adeseye ya rike ministan ayyuka ne a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, Legit.ng ta tattaro.

Sanata Ogunlewe ya bayyana haka ne a jiya Lahadi 30 ga watan Yuli yayin hira da gidan talabijin na Channels.

Asali: Legit.ng

Online view pixel