Tashin Hankali Yayin da PDP Ta Dakatar Da Shugaban Matasa Saboda Ya Zargi Saraki

Tashin Hankali Yayin da PDP Ta Dakatar Da Shugaban Matasa Saboda Ya Zargi Saraki

  • Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta dakatar da shugaban matasanta na jihar Kwara
  • Kwamitin aiki na PDP ya dakatar da Haliru Dansoho Mahmoud, har sai baba ta gani saboda zargin da ya yi wa Bukola Saraki
  • Mahmoud ya zargi Saraki da taka rawar gani da bai dace ba yayin zaben 2023 wanda a cewarsa shine ya shafi sakamakon PDP a jihar

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kwara ta dakatar da Haliru Dantsoho Mahmoud, shugaban matasanta, saboda furucin da ya yi a kan tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, shugaban matasan ya zargi tsohon shugaban majalisar dattawan da taka rawa da bai dace ba a babban zaben 2023.

An dakatar da shugaban matasan PDP a Kwara a kan Bukola Saraki
Tashin Hankali Yayin da PDP Ta Dakatar Da Shugaban Matasa Saboda Ya Zargi Saraki Hoto: Abubakar Bukola Saraki
Asali: Facebook

Shugaban matasan PDP a Kwara ya zargi Saraki da taka rawa wajen faduwarsu a zaben 2023

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Fusata, Ta Dakatar da Shugaban Matasan Jam'iyyar a Jihar Arewa Kan Abu 1

A cewar Mahmoud, abun da Saraki ya aikata ya bayar da gudunmawa a sakamakon PDP a zaben da aka yi a jihar, rahoton Daily Trust.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin PDP, Tunji Moronfoye, ya ce kwamitin aiki na jam’iyyar a jihar sun hadu a ranar Talata, 22 ga watan Agusta, sannan sun samu wani rahoto daga wani kwamitin ladabtarwa, wanda aka kafa domin duba zargin shugaban matasan.

“Rahoton da aka samu daga kwamitin ladabtarwa ya nuna karara cewa shugaban matasan jam’iyyar a jihar yana da laifi a kan dukkan tuhume-tuhume da mambobin jam’iyyar da suka shigar da kara gaban shugabancin jam’iyyar a jihar suke yi masa. Bayan duba rahoton kwamitin ladabtarwan, kwamitin SWC na jam’iyyar ya yanke shawarar dakatar da shugaban matasan na jihar har sai baba ta gani.”

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Makinde Da Sauran Yan G5 Sun Yi Gum Yayin da Wike Ya Kama Aikin Minista a Gwamnatin APC

Masomin fadawar PDP a rikici

Jam’iyyar PDP ta fada rikici tun zaben 2023, kuma ta abun ya fara ne tun da Atiku Abubakar ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Atiku ya kayar da Saraki a zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar amma sai ya zamana tsohon shugaban majalisar dattawan ya mara masa baya.

PDP ta yi watsi da rade-radin dakatar da Saraki

A wani labarin, mun ji a baya cewa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Kwara a ranar Asabar, 8 ga watan Yuli, ta karyata cewa tana shirin dakatar da Sanata Bukola Saraki.

Saraki ya kasance tsohon gwamnan jihar Kwara sau biyu kuma ya yi shugaban majalisar dattawan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel