“Makirci Ne”: PDP Ta Yi Watsi Da Rade-Radin Dakatar Da Saraki

“Makirci Ne”: PDP Ta Yi Watsi Da Rade-Radin Dakatar Da Saraki

  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ba da tabbacin cewa ba za ta dakatar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ba
  • PDP reshen jihar Kwara ce ta bayar da tabbacin a wata sanarwa dauke da sa hannun manyan jiga-jigan jam'iyyar buyu: Babatunde Mohammed da Abdulrazaq Lawal
  • Mohammed da Lawal sun ce masu yada labaran karya game da dakatar da Saraki makirci kawai suke kullawa

Ilorin, jihar Kwara - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Kwara a ranar Asabar, 8 ga watan Yuli, ta karyata cewa tana shirin dakatar da Sanata Bukola Saraki.

Saraki ya kasance tsohon gwamnan jihar Kwara sau biyu kuma ya yi shugaban majalisar dattawan Najeriya.

Bikola Saraki
“Makirci Ne”: PDP Ta Yi Watsi Da Rade-Radin Dakatar Da Saraki Hoto: Abubakar Bukola Saraki
Asali: Facebook

'Ba a fahimci sakamakon ganawar da aka yi a baya-bayan nan ba': PDP reshen Kwara

Kara karanta wannan

Muje zuwa: An kai karar Abba Gida-Gida Amurka, China da EU kan gallazawa Kanawa

Legit.ng ta fahimci cewa an gudanar da babban taro na mambobin jam'iyyar PDP a jihar Kwara a ranar Asabar, 1 ga watan Yuli. Bayan taron, sai aka fara yada jita-jitan cewa kwamitin aiki na jam'iyyar ya yanke shawarar hukunta Saraki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai kuma, wata sanarwa da PDP reshen Kwara ta fitar dauke da sa hannun shugaban jam'iyyar na jihar, Babatunde Mohammed da sakatarenta, Abdulrazaq Lawal; sun bukaci mambobin jam'iyyar da magoya bayanta da su kwantar da hankalinsu tare da jingine rade-radin dakatar da babban dan siyasar na Kwara.

Sun yi bayanin cewa an yi wa babban taron da aka kira a ranar Asabar, 1 ga watan Yulin 2023 domin sake duba sakamakon zaben 2023 "gurguwar fahimta ko kuma dai wasu magauta ne suka fassara shi baibai".

Sanarwar ta ce:

Kara karanta wannan

Kwamitin Bincike Ya Bayyana Abinda Yakamata Ya Faru Da Mmesoma Ejikeme Bayan Ta Kara Makin JAMB

“Muna kira ga yan jam’iyyarmu da magoya bayanmu da su kwantar da hankalinsu tare da jingine batun dakatar da shugabanmu, Sanata Abubakar Bukola Saraki da mambobin kwamitin aiki na jihar suka yi kamar yadda wasu mutane ke yadawa da nufin kawo rashin aminci a jam'iyyar."

Kotu ta dakatar da gayyatan da aka yi wa Ganduje kan bidiyon dala

A wani labari na daban, kotu ta hana hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano (PCACC) gayyata ko cin zarafin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje kan bidiyon da ake zarginsa da karbar dala.

Hukumar PCACC a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli, ta sanar da cewar ta gayyaci tsohon gwamnan don ya amsa wasu tambayoyi kan binciken da take yi a kan bidiyon dala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel