Tsohon Minista Shagari Ya Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC

Tsohon Minista Shagari Ya Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC

  • Jam'iyyar PDP ta sake rasa wani babban jigonta, Mukhtar Shehu Shagari, wanda ya sauya sheka zuwa APC a jihar Sokoto
  • Shagari ya rike mukamin ministan albarkatun ruwa a karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kuma ya taba mataimakin gwamna a jihar
  • An daura laifin sauya sheka da Shagari ya yi zuwa APC kan PDP, inda aka zargi jam'iyyar adawa da yi masa rashin adalci

Jihar Sokoto - Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya dauki sabon salo yayin da Barista Mukhtar Shehu Shagari, dan jam’iyyar daya da ya rage a jihar Sokoto ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Shagari wanda ya kasance tsohon ministan albarkatun ruwa a gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya karbi katin shaidar zama dan APC daga hannun sakataren jam'iyyar, Abubakar Yabo a gaban sauran shugabannin APC a jihar, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: An Nemi Tinubu Ya Dakatar Da Wike, Umahi Da Sauran Tsoffin Gwamnoni Daga Karbar Fansho

Muktar Shehu Shagari ya sauya sheka zuwa APC
Tsohon Minista Shagari Ya Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC Hoto: APC Nigeria
Asali: Twitter

Shagari ministan albarkatun ruwa mafi dadewa a majalisar tsohon shugaban kasa Obasanjo mafi dadewa ya kasance dan gani kashenin PDP kuma ya shafe sama da shekaru 25 a cikin jam'iyyar.

Dalilin da yasa Shagari ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Rahoton ya kuma ce wadanda suka magantu a kan ficewar da tsohon ministan ya yi zuwa APC sun daura laifin kan jam'iyyar na kasa kan kin yi wa Shagari adalci duk da biyayyarsa ga shugabancin jam'iyyar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sun ce duk wadanda suka yi zamani da tsohon Ministan a PDP sun dade da ficewa daga jam’iyyar ciki harda Alhaji Atiku Abubakar wanda ya koma ACN da APC kafin daga bisani ya dawo tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP neman tikitin shugaban kasa.

Yabo ya tabbatar da cewar tsohon ministan kuma tsohon mataimakin gwamnan na Sokoto ya karbi katin shaidar zama dan jam'iyyar a jihar, yana mai cewa a yanzu ya zama cikakken dan APC a jihar.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Shugaban Nijar Ya Bude Baki, Ya Fadi Shekarun da Zai Yi kan Mulki

Atiku vs Tinubu: Jigon PDP ya fadi wanda kotun zabe za ta ba nasara

A wani labarin, mun ji cewa Muhammed Kadade, shugaban matasan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya bukaci kotun zaben shugaban kasa da ta ayyana dan takarar jam'iyyarsa, Atiku Abubakar, a matsayin wanda ya lashe zaben 2023.

Kadade ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a, 18 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel