Shehu Sani Ya Ce A Gwamnatin Buhari Ne Aka Fi Sace Kudin Najeriya Da Ke Asusun Waje

Shehu Sani Ya Ce A Gwamnatin Buhari Ne Aka Fi Sace Kudin Najeriya Da Ke Asusun Waje

  • Sanata Shehu Sani ya bayyana gwamnatin da aka fi satar kuɗaɗen ajiya na ƙasashen waje a cikinta
  • Shehu Sani ya ce a lokacin Buhari ne aka yashe kuɗaɗen asusun Najeriya na waje fiye da kowace gwamnati
  • Sai dai tsohon sanatan ya ce mutum ɗaya ba zai iya wannan aika-aika ta yashe kuɗaɗen shi kaɗai ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya Sanata Shehu Sani, ya yi tsokaci gameda da gwamnatin da aka fi yashe kuɗaɗen Najeriya da ke asusunta na waje.

Ya ce a bayyana abubuwa suke kan gwamnatin da ta fi kowace sace kuɗaɗen ajiyar Najeriya.

Shehu Sani ya fadi gwamnatin da aka fi satar kuɗaɗen Najeriya a cikinta
Shehu Sani ya ce a gwamnatin Buhari ne aka fi satar kuɗaɗen Najeriya da ke asusun waje. Hoto: Shehu Sani
Asali: Facebook

Shehu Sani ya ce a gwamnatin Buhari aka fi satar kuɗaɗen

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumunta ta X, Shehu Sani ya ce gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta zarce kowace yashe kuɗaɗen Najeriya da ke ma'ajiyar ƙasar ta waje.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Emefiele Ya Isa Kotu Domin Fuskantar Tuhume-Tuhumen Da Ake Yi Ma Sa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai Sanata Shehu Sani ya ce yana kokonta cewa mutum ɗaya zai iya yin duka satar shi kaɗai ba tare da taimakon wasu ba.

Shehu Sani ya yi martani kan nadin Matawalle da Tinubu ya yi

A baya Legit.ng ta kawo rahoto kan martanin da Sanata Shehu Sani ya yi dangane da naɗin tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle matsayin ƙaramin ministan tsaro da Shugaba Bola Tinubu ya yi.

Matawalle dai yana cikin mutane 45 da Bola Ahmed Tinubu ya naɗa ministoci biyo bayan tabbatar da su da Majalisar Dattawan Najeriya ta yi a kwanakin baya.

Shehu Sani ya ƙalubalanci Tinubu kan cewa ba tsohon soja mai ƙwarewa kan harkokin tsaro ya kamata a bai wa muƙamin ba wai Matawalle ba.

Kara karanta wannan

Masanin Tattalin Arziƙi Ya Fadi Abinda Zai Faru Idan Ministocin Tinubu Suka Fara Aiki

Shehu Sani ya caccaki Tinubu kan tura dakaru Nijar

A wani rahoto na daban da Legit.ng ta yi, tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya ya caccaki Shugaba Bola Tinubu da ƙungiyar ECOWAS kan shirin da suke yi na tura dakarun yaƙi Nijar.

Shehu Sani ya roƙi Tinubu da ƙungiyar ta ECOWAS da su yi taka tsantsan domin gudun kada su jefa Najeriya cikin yaƙi.

Ya ce matakan diflomasiyya da ECOWAS ta ɗauka a farko, su ya kamata ta ci gaba da bi wajen samun abinda ake so.

Asali: Legit.ng

Online view pixel