“Kada Ku Jawo Ma Na Yaki”, Shehu Sani Ya Caccaki Tinubu Da ECOWAS Kan Matakin Soji

“Kada Ku Jawo Ma Na Yaki”, Shehu Sani Ya Caccaki Tinubu Da ECOWAS Kan Matakin Soji

  • Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya aikawa Tinubu da sauran shugabannin ECOWAS saƙo
  • A saƙon da ya wallafa a kafar sada zumunta, ya buƙaci ECOWAS da kar ta jefa 'yan Najeriya cikin yaƙi
  • Ya ce matakin da ECOWAS ke shirin ɗauka a yanzu ya saɓa da alƙawarin da ta yi a baya na bin hanyoyin diflomasiyya

Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya turawa Shugaba Tinubu, kuma shugaban ECOWAS muhimmin saƙo.

Shehu ya buƙaci Tinubu ya yi taka tsantsan da irin matakan da zai ɗauka dangane da batun juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar.

Shehu Sani ya aike da muhimmin saƙo ga Tinubu da ECOWAS
Shehu Sani ya caccaki Tinubu da ECOWAS kan matakin da suke shirin ɗauka. Hoto: Shehu Sani, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shehu Sani ya caccaki umarnin da ECOWAS ta ba sojoji

Bayan gabatar da taro a Abuja ranar Alhamis, 10 ga watan Agusta, ƙungiyar ECOWAS ta bai wa sojojinta umarnin ɗaura ɗamarar yaƙi kan yiwuwar afkawa sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.

Kara karanta wannan

Shugaban Kwaddibuwa Ya Ayyana Sojojin Nijar a Matsayin 'Yan Ta'adda, Ya Fadi Abinda Ya Kamata a Yi Mu Su

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake mayar da martani kan wannan umarni na ECOWAS ta shafinsa na Twitter, Shehu Sani ya roƙi Tinubu da ƙungiyar da kar su jefa Najeriya cikin yaƙi.

Ya ce matsayar da ECOWAS ta ɗauka a farko ta amfani da diflomasiyya, ta saɓa da matakin da ta ɗauka a yanzu na ƙoƙarin amfani da ƙarfin soji.

Yan Najeriya sun yi martani kan saƙon na Shehu Sani

'Yan Najeriya da dama da ke bibiyar tsohon sanatan, sun yi martani dangane da wannan shawara da ya ba da.

@YakubuNe ya ce:

“Girke sojojin ko ta kwana ba tunani ba ne mai kyau, ba ma bukatar ɗaukar matakin soji kwata-kwata a kan nijar.”

@TonyeBarcanista ya ce:

“Shugaba Tinubu ba shi da hurumin tura dakarun Najeriya tare da na ECOWAS tunda Majalisar Dattawa ba ta yarda ba. Za a iya tsige shi daga kan kujera idan ya matsa kan dole sai sun je.”

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: ECOWAS Ta Aike Da Zazzafan Gargadi Zuwa Ga Kasar Rasha

@MissPearls ta ce:

“Sun yi baki biyu kam. Sai su tura 'yan uwansu zuwa wurin yaƙin, sannan su tabbatar abin bai shafi farar hula ba. Taron mayaudara kawai.”

Jigon PDP ya faɗawa ECOWAS muhimman abubuwa 9 kan Nijar

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan wasu muhimman abubuwa guda 9 da jigon PDP, Daniel Bwala, ya faɗawa ECOWAS.

Ya ce ƙoƙarin dawo da dimokuraɗiyya a Nijar ba wani abu ba ne ƙarami da zai yiwu a yi shi cikin gaggawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng