Ko Kwankwaso Bai Isa Hana Mu Bin Tafarkin Kwankwasiya Ba, Dan A Mutun Jar Hula Ya Shiga Jazaba

Ko Kwankwaso Bai Isa Hana Mu Bin Tafarkin Kwankwasiya Ba, Dan A Mutun Jar Hula Ya Shiga Jazaba

  • Wani matashi a Kano ya bayyana cewa su fa irin tafiyar da suke a cikin darikar Kwankwasiya ba na wasa ba ne
  • Matashin mai suna Murad Faisaal ya ce ko wanda ya kirkiri tafiyar bai isa hana su bin darikar ba yadda suka rungume ta
  • Ya ce itafa Kwankwasiya ra'ayi ce kuma siyasa duk wanda yake aibata su akan haka to lallai ya jahilci sanin makamar rayuwa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Darikar Kwankwasiya a jihar Kano kullum kara yaduwa take musamman a tsakanin matasa inda wasu suka dauki darikar kamar wata bangare a rayuwarsu.

A jihar Kano kowa yasan yadda matasa ke nuna goyon bayansu ga Kwankwasiya wanda suke daukarsa a matsayin jagorar siyasar jihar.

Ko Kwankwaso Bai Isa Hana Mu Bin Tafarkin Kwankwasiya Ba, Dan A Mutun Jar Hula Ya Yi Bayani
Darikar Kwankwasiyya Kullum Kara Habaka Take A Kano Musamman A Tsakanin Matasa. Hoto: Murad Faisal/ Rabiu Kwankwaso.
Source: Twitter

Wani matashi mai suna @elfaisaal ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya ce tsabar yadda ya dauki Kwankwasiya a yanzu babu mai iya hana shi binta.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Yi Wa Samarinta 3 Dabara, Sun Zo Gaba Daya Sun Tayata Kwashe Kaya Zuwa Sabon Gida

Dan a mutun jar hula ya bayyana yadda yake ji da Kwankwasiya

Matashin ya kara da cewa hatta shi kansa Kwankwaso bai isa ya hana shi bin darikar Kwankwasiya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"Ko Kwankwaso da kansa bai isa ya hana mu bin darikar Kwankwasiya ba, ta fi karfinsa a matsayinsa na dan Adam.
"Wannan shi ne abu daya da akidar ci gaba kenan, da zarar an kirkireta, za ta zarta wanda ya kirkiro ta, ta wuce maganar gadoji da iyakoki, kullum ninkuwa take."

Ya kara da cewa ya kamata mutane su sani ita fa Kwankwasiya ra'ayi ce kuma siyasa.

Ya ce masu aibata su kan Kwankwaso suna bata lokacin su ne

Ya ce duk wani zagi da aibata su ba zai hana komai ba, don kawai an samu bambancin ra'ayi.

Inda ya ce masu aibata su kawai jahilci ne ke damunsu da rashin sanin alfanun rayuwa.

Kara karanta wannan

“Dukana Take Yi”: Miji Ya Maka Matarsa a Kotu, Ya Fadi Wahalar Da Yake Sha a Hannunta

Ya kara da cewa:

"Ita fa Kwankwasiyya-r nan ra'ayi ce. Kuma siyasa ce.
"Zagi da aibata mu, saboda mu na bin layin siyasar da ba kwa bi, sakamakon saɓanin ra'ayi.
"Wannan tsananin rashin wayewa ne da jahiltar sanin makamar rayuwa mai alfanu. Ku sake tunani."

Kano: Kwankwaso Ya Yi Martani Kan Zargin Juya Gwamnatin Abba Gida Gida

A wani labarin, jagoran siyasar jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ya musanta rade-radin da ake cewa shi ya ke juya gwamnatin Abba Gida Gida.

Kwankwaso ya ce abin da yanzu talakawa ke bukata kawai shi ne su gani kasa a na ayyukan ci gaba.

Ya bayyana yadda lokacin mulkinsa har rokonsa ake ya rusa gida don biyan kudin diyya saboda sun ninka kudin har sau goma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.