“Duka Take Yi Mun Kamar An Aiko Ta”: Miji Ya Maka Matarsa a Kotu, Ya Fadi Wahalar Da Yake Sha a Hannunta

“Duka Take Yi Mun Kamar An Aiko Ta”: Miji Ya Maka Matarsa a Kotu, Ya Fadi Wahalar Da Yake Sha a Hannunta

  • Magidanci ya maka matarsa a gaban kuliya saboda bakar azabar da take gana masa a zamansu
  • Mutumin ya bayyana cewa matarsa na yi masa mugun duka kamar an aiko ta sannan ta kona masa tufafinsa
  • Baya ga haka, ya zargi matar tasa da yi masa yankan baya ta hanyar yin sharholiya da daya daga cikin abokansa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani magidanci ya maka matarsa a gaban kotu saboda irin azabar da take gana masa yake shanyewa a gidan aurensu.

Duk da kasancewar maigidanta, mutumin ya bayyana cewa matar na matukar wahalar da shi tare da gana masa azaba iri-iri.

Sandar kotu
“Duka Take Yi Mun Kamar An Aiko Ta”: Miji Ya Maka Matarsa a Kotu, Ya Fadi Wahalar Da Yake Sha a Hannunta Hoto: NAN.
Asali: UGC

Da yake bayyana abubuwan da take yi masa a cikin wani bidiyo da shafin @yabaleftonline ya wallafa a Twitter, mutumin ya yi bayanin cewa matar na yawan dukan shi a duk lkokacin da ta ji yin hakan.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Dan Najeriya Ya Baje Kolin Janareto Mara Amfani Da Fetur, Da Hasken Rana Yake Aiki Kuma Baya Kara

Ya tuna wani al'amari da ya faru inda ta tambaye shi dalilin da yasa baya rokonta gafara kamar yadda mahaifinta yake yi a duk sanda mahaifiyarta take dukansa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai kuma, ya nuna cewa watakila mahaifinta na da karfin da zai iya jure irin haka, sabanin shi da ba zai iya ba.

Matata na aikata masha'a da abokina, magidanci ya koka

Bugu da kari, mutumin ya bayyana cewa a lokuta da dama, matarsa ta sa lalata dukkanin kayan da ya mallaka, inda take barinsa ba tare da kayan sanyawa zuwa wajen aiki ba, inda hakan ke sanya shi aron kaya don dole.

Hakazalika, ya zargi matar da aikata masha'a da daya daga cikin abokansa.

Yan Najeriya sun yi martani ga wannan abu da mutumin ya bayyana suna masu bayyana ra'ayoyinsu a sashin sharhi.

Kara karanta wannan

“Na Rasa Matata Da Yara 5”: Matashiy Ya Taimaki Wani Tsoho Da Ke Yawon Bara a Titi a Bidiyo Mai Tsuma Zuciya

Jama'a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin da jama'a suka yi a kasa:

@Irunnia_ ta yi martani:

"Kalli yadda kowa ke yi wa mutumin dariya yanzu kuma ya zama abun dariya. Idan aka sauya jinsin, da Twitter ya kama da wuta yau."

@_Gabri3llaa ta ce:

"Baaba! Wato wasu mata na dukan mazajensu suma? Wannan rayuwar kooo."

@colesshutterr ya ce:

"Lol idan da za a sauya lamarin Twitter ba za ta samu zaman lafiya ko kadan ba a yau."

@chi4real___ ta ce:

"Idan da mutumin ne ke dukan matar yanzu, za su caccake shi sannan su kira shi da sunaye."

@chi_agozie7 ya ce:

"Ba zan kalli bidiyon nan ba saboda ban yarda cewa mace za ta iya dukan mijinta ba."

Budurwa ta yi wa maza 2 alkawarin aure, dayan ya bayyana a ranar bikinta, ya hana ta sukuni

A wani labarin kuma, wani matashi dan Najeriya mai suna @StFrakingKezy ya wallafa bidiyoyi biyu na wani al'amari da ya yi ikirarin ya faru a yankin Apete ta Ibadan a ranar Asabar, 8 ga watan Yuli.

@StFreakingKezy ya ce amaryar wacce ta yi alkawarin auren maza biyu ta cika da mamaki. Daya daga cikin mazajen da ta yi wa alkawarin aure ya bayyana a ranar daurin aurenta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel