Kano: NLC Za Ta Shiga Kafar Wando Daya Da Abba Gida Gida Kan Tsayar Da Albashin Ma’aikata 10,000

Kano: NLC Za Ta Shiga Kafar Wando Daya Da Abba Gida Gida Kan Tsayar Da Albashin Ma’aikata 10,000

  • Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) reshen jihar Kano za ta shiga kafar wando da gwamnatin jihar Kano kan dakatar da albashin ma'aikata
  • Shugaban kungiyar a jihar, Kabiru Inuwa shi ya bayyana haka inda ya ce za su yi wata ganawa a ranar Litinin 3 ga watan Yuli mai kamawa
  • Abba Kabir Yusuf a baya ya ba da umarnin dakatar da albashin ma'aikata wadanada ya ke zargin an dauke su ba bisa ka'ida ba a jihar

Jihar Kano - Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) reshen jihar Kano ta tsoma baki kan matsalar tsayar da albashin ma'aikata a jihar.

Ma'aikatan da abin da shafa sun kai akalla 10,000 da gwamnatin jihar ta tsayar musu albashi.

NLC ta shiga kafar wando daya da Abba Gida Gida kan dakatar da albashin ma'aikata a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf Na Kano: Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Idan ba a manta ba, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin tsayar da albashin ma'aikata da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya dauka.

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje Ya Koka Kan Dakatar da Albashin Ma'aikata Sama da 10,000, Ya Tona Wani Sirrin Abba Gida Gida

Kungiyar ta ce za su gana tsakaninsu kafin samun Abba Gida Gida akan matsalar albashin

Shugaban kungiyar a jihar, Kabiru Inuwa ya bayyana cewa za su gudanar da wata ganawa don samo mafita akan matsalar, Vanguard ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"Za mu samo mafita akan wannar matsalar a ganawar da zamu yi a ranar Litinin.
"A yayin tattaunawar, wadanda abin ya shafa za su rubuto matsalolinsu ga kungiya don nemo mafita.
"Za mu shiga takun saka da gwamnati da zarar mun samar da mafita a tsakanin mu."

Abba Gida Gida ya dakatar da albashin ne bisa zargin rashin bin ka'ida wurin daukar su aiki a Kano

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya dakatar da biyan albashin ma'aikatan har sai lokacin da aka gama tantance hanyar da aka bi wurin ba su aikin.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Peter Obi Ya Zauna da Musulmai, Ya Ba Su Kudi a Gyara Masallatai

Abba Kabir na binciken duk wasu aikace-aikace da tsohon gwamna Ganduje ya yi a jihar don tsabtace su tun bayan hawanshi karagar mulki a jihar, cewar rahotanni.

Gwamna Abba Kabir Na Kano Ta Biyawa Dalibai 55,000 Kudin Jarrabawar NECO

A wani labarin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da biya wa dalibai kudaden jarrabawar NECO a jihar.

Gwamnan ya ce wannan mataki ne na inganta harkar ilimi a jihar da ke faman durkushewa.

A karshe ya roki daliban da su dage don samun sakamako mai kyau saboda gwamnati da iyayensu su yi alfahari da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel