Abba Gida Gida Ya Karya Alkawari, Ya Jawo Yaronsa Ya Ba Shi Mukami a Gwamnati

Abba Gida Gida Ya Karya Alkawari, Ya Jawo Yaronsa Ya Ba Shi Mukami a Gwamnati

  • Abba Kabir Yusuf ya ba Arc. Ahmad A. Yusuf shugabancin hukumar kula da tarihi da al'adu
  • Da ake rantsar da shi a matsayin Gwamna, ya ce iyalinsa ba za su shiga harkokin gwamnati ba
  • Ana zargin Dr. Abdullahi Ganduje da yin mulki da ‘yan gidansa a lokacin da yake rike da karaga

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Ana zargin sabon Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da yin magana biyu a dalilin mukamin da ya ba wani da yake ‘da a wajensa.

A ranar Talata, labari ya fito daga Daily Trust cewa Ahmad A. Yusuf wanda ya samu mukami a gwamnatin Kano, ‘danuwan Mai girma Gwamna ne.

A karshen makon jiya ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada Ahmad Yusuf a matsayin Babban Sakataren hukumar tarihi da al’adun Kano.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Nada Kwamiti, Za a Binciki Shekaru 4 da Tsohon Gwamna Ya Yi

Abba Gida Gida
Abba Kabir Yusuf da Arc. Ahmad A. Yusuf Hoto: Sanusi Bature Dawakin-Tofa
Asali: Facebook

Inda abin maganar ta ke

Abin da ya jawo korafin shi ne sabon Shugaban hukumar ya na cikin ‘ya ‘yan yayan Gwamnan da aka fi sani da Abba Gida Gida a kusan duk Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bugu da kari, jaridar ta ce wannan Bawan Allah ya taso ne a hannun Abba Kabir Yusuf.

Abin bai tsaya a nan ba, matashin ya na amfani da sunan sabon Gwamnan domin shi ya rike shi, kwatsam kuma sai aka ji ya samu kujera a gwamnati.

Abin da ya haddasa surutun shi ne Abba Gida Gida ya yi alkawari cewa a matsayin Gwamna, iyalinsa ba za su rika shiga cikin harkokin gwamnati ba.

Kwatsam sai aka ji wani daga cikin dangi kuma na-kusa da Gwamnan ya samu mukami.

Abin yabo ko abin suka?

Legit.ng Hausa ta fahimci mutane da-dama sun yaba da nadin da Gwamnan Kano ya yi a hukumar tarihi da al’adun, musamman ganin ya dauko matashi.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba Ya Ɗau Zafi, Ya Umarci Dukkan Kwamishinonin da Ya Naɗa Su Bayyana Dukiya Nan Take

Wasu sun bayyana cewa Ahmad Yusuf mutum ne wanda ya san tarihin jihar Kano kuma yake goyon-bayan NNPP, duk da a fannin zane ya yi digirinsa.

Sakataren yada labaran Gwamnan, Sanusi Dawakin Tofa ya ce mahaifin Sakataren shi ne Abba Yusuf wanda a yau shi ne Magatakardar masarautar Kano.

An nada Hadimai, an zabi Kwamishinoni

Bayan makonni uku a mulki, a jiya aka samu labari Gwamnan Kano ya tura sunayen kwamishinoni 19 ga majalisar dokokin Jiha domin a tantance su.

An san cewa an nnada Arc. Ahmad A. Yusuf ne tare da Ado Kankarofi wanda ya zama mataimakin shugaban hukumar KARMA mai gyaran tituna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel