Gwamnan Arewa Ya Nada Kwamiti, Za a Binciki Shekaru 4 da Tsohon Gwamna Ya Yi

Gwamnan Arewa Ya Nada Kwamiti, Za a Binciki Shekaru 4 da Tsohon Gwamna Ya Yi

  • Agbu Kefas ya nada wani kwamiti na musamman da zai binciki abubuwan da aka yi a jihar Taraba
  • Kwamitin zai binciki duka hukumomi da ma’aikatun Jiha, aikin zai shafi 2019 ne har zuwa 2023
  • SSG ya ce Polycarp Iranius zai jagoranci wannan aiki, shi ne jami’in binciken kudin gwamnati

Taraba - Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ya kafa wani kwamitin mutum tara da zai yi bincike kan abubuwan da su ka faru tun daga 2019.

Kamar yadda labari ya zo daga Punch, Mai girma Agbu Kefas ya umarci ayi binciki domin ganin yadda aka tafiyar da hukumomin jihar Taraba.

A makon nan Gwamna kefas ya sauke dukkanin shugabannin da ke kula da hukumomi da ma’aikatun da Darius Ishaku ya nada a ofis.

Gwamnan Taraba, Kefas Agbu
Gwamnan Taraba, Kefas Agbu ranar rantsuwa Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Gwamnan ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar a garin Jalingo ta bakin sakataren gwamnati, Cif Gibeon-Timothy Kataps a yammacin Litinin.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida Ya Karya Alkawari, Ya Jawo Yaronsa Ya Ba Shi Mukami a Gwamnati

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwar SSG, Gibeon-Timothy Kataps

"Mai girma Gwamnan Taraba, Dr. Agbu Kefas ya amince da sauke da shugabannin da ke kula da hukumomi da ma’aikatun da ke karkashin jihar.
An ruguza shugabannin ne ba tare da bata lokaci ba kuma wadanda abin ya shafa za su damka duk wasu kaya da kadarorin gwamnati da ke hannunsu zuwa ga jami’in da ya fi matsayi a wadannan hukumomi ko ma’aikatu nan da sa’o’i 48.
Sannan Gwamna ya amince da kafa kwamitin mutum tara da zai binciki ayyukan da aka yi a hukumomi da majalisun Taraba daga 2019 zuwa 2023.

Jaridar ta ce kwamitin binciken ya na karkashin jagorancin mai binciken kudi, Polycarp Iranius.

Iranius, da ‘yan kwamitinsa mai kunshe da kwararrun ma’aikata za su duba yadda kudi su ka rika shigowa da kuma fitarsu a cikin shekarun hudu.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamnan Arewa Ya Yi Shiga Mai Ban Mamaki, Ya Kai Ziyarar Bazata Wani Asibiti a Keke Napep

Sannan kwamitin zai yi wa gwamnati bayanin kokarin da hukumomin su ke yi, a karshe za su bada shawarar hanyar da za abi domin kawo gyara.

Ritaya a gidan soja

Sababbin Hafsoshin za su samu karin girma, amma an ji labari cewa za a tattara ‘yan bayansu ayi masu ritaya, za a rasa Sojoji fiye da 160 watanni shida.

Sojoji da-dama za su sake ajiye khaki watanni kadan bayan ritayar da aka yi wa manyan jami’an tsaron kasar da su ka yi shekaru 35 su na kan aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel