Motocin Alatu na Miliyoyin Kudi da Wizkid ya Saya tun Bayan Fara Waka

Motocin Alatu na Miliyoyin Kudi da Wizkid ya Saya tun Bayan Fara Waka

Mawakin da ya fi kowa kudi a Najeriya, Ayodeji Ibrahim Balogun da aka fi sani da Wizkid ya tara makudan kudi da yawansu ya kai N44.6bn a shekarar 2024.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Ficen da Wizkid ya yi a Najeriya da sauran sassan duniya ya sa mawakin ya sayar da wakokin da ya ke yi, da ma yi wa wasu manya-manyan kamfanoni talla.

Wizkid
Wizkid da ya fi kowane mawaki kudi a Najeriya na da jerin motocin alatu 15 Hoto: Wizkid
Asali: Facebook

Yadda Wizkid yake samun kudi

Baya da wadannan sana’o’i na waka da talla, Wizkid na da shagon sayar da kaya a wasu yankunan Birtaniya da kasar Amurka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

‘Yan autan gwamnonin jihohi da aka yi a Najeriya tun daga zaben 1999 zuwa 2023

Wannan ya taimaka har ya zama mafi arziki daga mawakan da Najeriya ke fariya da su a Afrika mai tarin dukiya da motocin alatu 15, kamar yadda Leadership News ta wallafa.

Motocin WizKid da yake ji da su

Ga jerin wasu daga motocin da Wizkid ya mallaka:

1. BMW X6 crossover

Wannan ce motar farko da mawakin ya mallaka daga farko-farkon fara wakarsa. Kudin motar ya kai N15m.

2. Lamborghini Urus

Wizkid ya sayi wannan hamshakiyar mota a shekarar 2018, kudinta ya kai N350m.

3. Porsche Panamera

Abin na Wizkid gaba-gaba ya dinga yi, domin bayan Lamborghini Urus, an hango mawakin da mota kirar Porsche Panamera wanda kudinta ya kai N60m.

4. Mercedes Benz V

A shekarar 2019, likkafar Wizkid ta ci gaba, inda ya sake sayen wata motar kirar Mercedes Benz V, ana sayar da motar akan N78m zuwa sama.

5. Mercedes-Benz

Mawakin da alama ya ji dadin motar, inda ya kara sayen Mercedes-Benz G-Wagon a kan N70m.

Kara karanta wannan

"Ko a jikina," Ministan Tinubu ya maida martani kan abubuwan da ke faruwa a Rivers

6. Porsche Cayenne

Daga baya shahararren mawakin ya kara sayen Cayenne a kan N18M.

7. Lamborghini Aventador

A shekarar 2019, mawaki Wizkid ya sayi Lamborghini Aventador a kan N600M.

8. Rolls Royce Cullinan

A shekarar 2021, fitaccen mawakin ya kara sayen mota ta biyu Rolls-Royce Cullinan N438m.

Ta yaya wizkid ya samu kudi?

Wizkid shahararren mawaki ne da ya yi fice wajen sayar da tikitin zuwa wakokinsa.

Ya samu kudi ta hanyoyi da dama bayan waka, kamar karbar talla daga kamfanoni .

Ga wasu daga kamfanonin da Wizkid ya yi aiki da su;

1. Wizkid & Pepsi

$300,000 shi ne kudin da Wizkid ya samu a aikin da ya yiwa kamfanin Pepsi a shekarar 2012.

Bayan shekara guda kamfanin lemon ya kara wa’adin kwangila da shekaru biyar.

2. Wizkid & MTN

Likkafar Wizkid ta daga a shekarar 2013, inda ya samu kwangilar zama jakadan MTN na shekara daya.

Kara karanta wannan

"An yi amfani da bam": Mutum 1 ya mutu da aka bankawa masallata wuta a Kano

Kudi masu tarin yawa mawakin ya samu a wannan aiki, wanda ya kai $115,000, daga baya MTN ta kara wa’adin kwangilar zuwa shekaru biyu, wanda ke nufin ya yi aikin shekara uku da kamfanin.

3. Wizkid & Ciroc

A shekarar 2018, matashin mawaki ya samu zama jakadan Croc kan kudi masu kauri, duk da ba a fadi nawa ne ba.

Kamfanin dai na sayar da giyar Vodka, wanda wasu ke ganin ya nuna irin farin jinin da mawakin ke da shi.

4. Wizkid da United Bank of Africa (UBA)

A shekarar 2019, Wizkid ya zama jakadan bankin UBA. Ya samu gwaggwaban kudi har $3,000,000.

Wannan aiki da ya yi ya kara masa karsashi a idon duniya, har ta kai ya samu karin tallace-tallace daga wasu kamfanonin.

5. Wizkid da Tecno Mobile

Daya daga kamfanonin da Wizkid ke yi wa talla akwai Tecno Mobile, inda ya zama jakadansu a shekarar 2020 a kan $150,000.

Kara karanta wannan

Babu Bahaushe ko 1: Jerin manyan mawaka 10 mafi arziki a Nigeria a 2024

Wizkid ya zama mawaki mafi arziki

A baya mun kawo mu ku labarin cewa Ayodeji Ibrahim Balogun Wizkid ya zama mawaki mafi arziki daga cikin mawakan Najeriya inda ya mallaki kudi da yawansu ya kai N44.6bn.

Rahotanni sun bayyana cewa Wizkid ya tara kudin ne ta hanyar sayar da wakokinsa har ta sahar spotify, da tallace-tallace da ya ke yi da kuma karbar jakadanci daga kamfanoni.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel