An Kame Matasan da Suka Yi Amfani da Bindigar Wasan Yara Wajen Sace Mota a Enugu

An Kame Matasan da Suka Yi Amfani da Bindigar Wasan Yara Wajen Sace Mota a Enugu

  • 'Yan sanda sun kame wasu matasa biyu da suka yi amfani da bindigar wasa wajen sace mota a jihar Enugu
  • An kwato wasu kayayyakin aikata laifi daga hannunsu tare da bayyana abubuwan da suka kwace a hannun mai motar
  • Ya zama ruwan dare sace mota ko wasu kadarori a cikin al'ummar Najeriya, lamarin da ke kara daukar hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Enugu - Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu aKudu maso Gabashin Najeriya ta ce ta kama wasu yara maza biyu da ake zargi da laifin fashi da makami a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Daniel Ndukwe ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren Juma’a 17 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta mayarwa Amurka $22,000 da wani dan Najeriya ya sata ta yanar gizo

An kama matasan da suka sace mota ta hanyar amfani da bindigar wasan yara
An kame matasa da suka sace mota a Enugu | Hoto: NPF
Asali: Facebook

Kakakin ya bayyana wadanda ake zargin da sunan Favor Akabue mai shekaru 18 da kuma Chiemezie Obayi mai shekaru 19 – dukkansu mazauna yankin Trans Ekulu a karamar hukumar Enugu ta Gabas a jihar, Premium Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda matasa suka aikata fashi da makami

Ya bayyana cewa, 'yan sanda sun samu labarin cewa, matasan sun yi amfani da bindigar wasan yara wajen kwacen mota kirar Honda da sanyin safiyar ranar 3 ga watan Mayu.

A cewarsa, lamarin ya auku ne a yankin Amaetiti-Akwu da ke yankin Achi a karamar hukumar Oji-River ta jihar, The Nation ta ruwaito.

Hakazalika, ya ce matasan sun kuma kwaci kudi da wayar hannu a mutumin da suka yiwa wannan mummunan aikin.

Yadda aka kai ga kwamushe matasan

Daga nan ne jami'an 'yan sanda suka dunguma don kai dauki, inda suka kai ga kame matasan bayan dogon tsere da suka yi dasu.

Kara karanta wannan

An yi garkuwa da babban malamin addini a Nigeria, 'yan sanda sun magantu

An kwace bindigogin wasan yara guda biyu, sirinji mai dauke da ruwan acid da kuma wasu kayayyakin aikata laifi.

Matasa a wasu yankunan Najeriya sun baci da barnar sace-sace da kuma daukar abin da ba nasu ba, musannan a 'yan shekarun nan.

Hargitsi ya tashi a Abuja tsakanin sojoji da 'yan kasuwa

A wani labarin, kun ji yadda wani hargitsi ya tashi tsakanin 'yan kasuwa da sojoji a wata kasuwar Abuja.

An ruwaito cewa, wasu bata-gari ne suka afkawa sojojin a cikin kasuwa, lamarin da ya dagula lissafi a cikinta.

Ya zuwa lokacin hada rahoton, ba a tabbatar da gaskiyar abin da ya jawo tashin hankalin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.