Ana Kishin Kishin, an Fara Neman Wanda Zai Karbi Kujerar APC a Hannun Ganduje

Ana Kishin Kishin, an Fara Neman Wanda Zai Karbi Kujerar APC a Hannun Ganduje

  • Biyo bayan kira a sauke Abdullahi Umar Ganduje, rade-radi na cewa fadar shugaban kasa ta fara kokarin sauke shi.
  • Haka zalika watakila an samu kwamitin da zai nemo sabon shugaban APC da zai maye gurbin Abdullahi Ganduje.
  • Har ilayau ana sa ran sabon shugaban da zai jagoranci APC NWC zai fito ne daga yankin Arewa.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Ana rade-radin fadar shugaban kasa ta fara yunkurin sauya Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyar APC na kasa.

Shugaban APc
APC za ta sauke Ganduje daga shugabanci. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Facebook

Yunkurin ya biyo bayan kiraye-kiraye da masu ruwa da tsaki da tsagin jam'yyar suka yi kwanakin baya a Najeriya.

Jaridar Leadership ta gano cewa fadar shugaban kasa ta na kokarin kafa kwamitin da za su nemo wanda zai rike muƙamin bayan sauke Ganduje.

Kara karanta wannan

Yayin da ake jita jitar sauya shi, Ganduje ya fadi abin da Tinubu ya yi da kowa ya gaza

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC: Su wanene 'yan kwamitin?

Rahotanni sun nuna cewa gwamnonin jam'iyyar APC da ke yankin Arewa ta tsakiya ne za a daura wa alhakin nemo wanda zai maye gurbin Ganduje.

Dama ma dai jam'iyyar ta ayyana cewa shugaban ta a wannan karon zai fito ne daga yankin Arewa ta tsakiya.

Bangaren da sabon shugaban APC zai fito

Sai dai wasu bayanan da suka fito daga fadar shugaban kasa sun nuna cewa sabon shugaban zai fito ne daga ɓangaren CPC, cewar Nigerian Bulletin.

CPC tana cikin jam'iyyun adawa da suka yi haɗaka wajen kafa jam'iyyar APC gabanin zaben 2015.

Korafin da aka yi kan Ganduje a APC

Daga cikin abubuwan da aka koka kan Ganduje akwai matsalolin da jam'iyyar ta samu a zabukan fitar da gwani a jihohin Edo da Ondo.

Kara karanta wannan

Kungiya ta wanke Ganduje daga zargin rashawa, ta kalubalanci gwamnatin Kano

Ciki har da abubuwan da suka biyo baya na bincikar gwamantinsa da gwamnatin Kano ta fara a kwanakin baya.

A wani bangaren kuma ana rade-radin cewa shirin dawowar Rabi'u Musa Kwankwaso jam'iyyar APC na daga cikin abubuwan da suka sa za a sauke Ganduje.

Ganduje ya ce APC ce mafita a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa duk da matsalar da shugaban APC ke ciki, ya tabbatar da cewa jam'iyyarsu ita ce kadai hanyar dakile matsalolin kasar.

Abdullahi Ganduje ya tabbatar da haka ne a lokacin da ya je jihar Gombe domin ayyukan cigaba inda ya ce APC ce kadai mafita a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel