Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Ɗan Majalisar Tarayya a Jihar Zamfara

Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Ɗan Majalisar Tarayya a Jihar Zamfara

  • Jam'iyyar APC ta tabbatar da dakatar da ɗan majalisar Kaura Namoda da Birnin Magaji, Honorabul Aminu Sani Jaji a jihar Zamfara
  • Sakataren APC na jihar, Alhaji Ibrahim Umar Dangaladima, ya ce kwamitin zartarwa ya amince da rahoton kwamitin ladabtarwa
  • An ɗauki wannaan matakin ne bisa zargin Jaji da cin amanar jam'iyyar APC da kuma rashin mutunta gayyatar da aka yi masa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) reshen jihar Zamfara ta dakatara da ɗan majalisar wakilan tarayya, Aminu Sani Jaji.

Jam'iyyar APC ta bayyana cewa ta ɗauki wannan matakin kan ɗan majalisar ne bisa zarginsa da cin amana da yi wa jam'iyya zagon ƙasa.

Kara karanta wannan

Cin Amana: Bayan caccakar ministocin Tinubu, APC ta dakatar da Sanata mai ci a jami'yya

Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje.
APC ta dakatar da Aminu Jaji, ɗan majalisar tarayya daga Zamfara Hoto: @Aminu_Jaji
Asali: Twitter

An dakatar da 'dan majalisa a APC

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, Sani Jaji, shi ne mai wakiltar mazaɓar Kaura Namoda/Birnin Magaji a majalisar wakilai ta ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren APC na jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Umar Dangaladima, ne ya sanar da haka yayin zantawa da manema labarai ranar Jumu'a, 17 ga watan Mayu.

Meyasa APC ta dakatar da Jaji?

Ibrahim Umar Dangaladim ya ce shugabannin jam'iyya na gundumarsa a Birnin Magaji sun dakatar da ɗan majalisar ne biyo bayan gano rashin gaskiyar da yake shukawa da rashin halartar tarurruka.

"Kwamitin ladabtarwa na mutum 7 ya bayar da shawarin a dakatar da shi saboda rashin mutunta gayyatar da kwamitin ya masa ba ɗaya ba kuma ba biyu.
"A halin yanzu kwamitin zartarwa na jiha ya yi nazari kan rahoton kwamitin ladabtarwa kuma ya amince da shawarwarin ɗaukar matakin dakatar da ɗan majalisar.

Kara karanta wannan

Sarkin Tikau, Alhaji Muhammadu Abubakar ya riga mu gidan gaskiya

"Duba da haka, kwamitin zartarwa na APC ta jihar Zamfara ya amince da dakatar da Honorabul Aminu Sani Jaji daga jam'iyyar."

- Ibrahim Umar Dangaladima

Wannan dai ya ƙara tabbatar da matakin da jam'iyyar APC reshen Birnin Magaji ta ɗauka kan Aminu Sani Jaji, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto

Jigon PDP ya koma APC a Osun

A wani rahoton kuma jam'iyyar PDP a jihar Osun a karkashin jagorancin Gwamna Ademola Adeleke ta rasa ɗaya daga cikin manyan kusoshinta

Alhaji Shuaib Oyedokun ya fice daga PDP kamar yadda ya bayyana a wasiƙar da ya miƙa wa shugannin jam'iyyar na Osun ranar Alhamis.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel