Abba Gida Gida Ya Aike da Sunayen Kwamishinoni 19 Ga Majalisar Dokokin Kano

Abba Gida Gida Ya Aike da Sunayen Kwamishinoni 19 Ga Majalisar Dokokin Kano

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya naɗa kwamishinoni 19 kuma ya tura sunayensu zuwa majalisar dokokin jihar
  • Kakakin majalisa, Isma'il Falgore, ya karanta sunayan kwamishinonin da mai girma gwamna ya aiko a zaman ranar Talata
  • Daga cikin waɗanda aka ji sunansu harda tsohon shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Ganduje da yayan Murtala Sule Garo

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ya fi shahara da Abba Gida-Gida, ya aike wa majasar dokokin jihar da sunayen mutanen da yake son naɗa wa kwamishinoni.

Jaridar Aminiya ta tattaro cewa gwamnan ya tura sunayen mutane 19 ga majalisar dokokin Kano domin tantance su gabanin ya naɗa su a matsayin kwamishinoni.

Zauren majalisar dokokin Kano.
Abba Gida Gida Ya Aike da Sunayen Kwamishinoni 19 Ga Majalisar Dokokin Kano Hoto: aminiya
Asali: UGC

Kakakin majalisar, Honorabul Yusuf Falgore, ne ya karanta sakon mai girma gwamna a zaman 'yan majalisar na yau Talata, 20 ga watan Yuni, 2023.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta Amince Abba Gida-Gida Ya Naɗa Wani Shehin Malami da Mace a Matsayin Kwamishinoni

Daga cikin waɗanda gwamnan ke son naɗa wa a matsayin kwamishinoni harda tsohon shugaban ma'aikata a gwamnatin Ganduje, Honorabul Ali Haruna Makoda.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka zalika Gwamnan ya tura da sunan Nasiru Sule Garo, yayan Murtala Sule Garo, ɗan takarar mataimakin gwamna a inuwar jam'iyyar APC a babban zaɓen 2023.

Honorabul Falgore, shugaban majalisar dokokin ne ya karanta sunayen da gwamman ya turo a cikin takardar.

Wani sashin takardar gwamnan ya ce:

"Duba da karfin ikon da kundin mulkin Najeriya ya bani, Na turo sunayen waɗan nan mutanen domin naɗa su a matsayin kwamishinoni idan majalisa ta sahale mun."

Jerin sunayen mutane da gwamnan ya naɗa kwamishinoni

Daily Trust ta tattaro muku cikakken jerin sunayen mutane 19 da gwamnan ya aike majalisa domin tantance su a matsayin kwamishinoni, ga su kamar haka:

1. Kwamaret Aminu Abdulsalam

Kara karanta wannan

Gwamnoni 11 Sun Ziyarci Tsohon Shugaban APC Da Ya Yi Murabus, Sun Roƙe Shi Alfarma 1 Tak

2. Honorabul Umar Doguwa

3. Honorabul Ali Haruna Makoda

4. Honorabul Abubakar Labaran Yusuf

5. Honorabul Danjuma Mahmoud

6. Honorabul Musa Shanono

7. Honorabul Abbas Sani Abbas

8. Hajiya Aisha Saji

9. Hajiya Ladidi Garko

10. Dakta Marwan Ahmad

11. Injiniya Muhd Diggol

12. Honorabul Adamu Aliyu Kibiya

13. Dakta Yusuf Kofar Mata

14- Honorabul Hamza Safiyanu

15- Honorabul Tajo Usman Zaura

16. Sheikh Tijjani Auwal

17. Honorabul Nasiru Sule Garo

18. Honorabul Haruna Isa Dederi

19. Honorabul Baba Halilu Dantiye.

Bashin N187bn: Hukumar EFCC Ta Tsare Tsohon Gwamnan Arewa Na PDP

A wani labarin na daban kuma Tsohon gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya shiga hannun hukumar yaki da rashawa EFCC.

Rahoto ya nuna cewa tun karfe 10:08 na safe tsohon gwamnan ya kai kansa ofishin EFCC kuma har yanzun yana tsare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel