Gwamna Aliyu Ya Yi Badda Kama, Ya Shiga Keke Napep Ya Kai Ziyarar Bazata Asibiti

Gwamna Aliyu Ya Yi Badda Kama, Ya Shiga Keke Napep Ya Kai Ziyarar Bazata Asibiti

  • Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sakkwato ya kai ziyarar ba zata Asibiti na musamman da ke cikin garin Sokoto a Keke Napep
  • Gwamnan ya yi badda kama yayin wannan ziyara ta tsawon awa huɗu kuma ya gano abubuwa da dama
  • Ya ce mutane sun kai masa ƙorafin mummunar lalacewar da Asibitin ya yi shiyasa ya zaɓi zuwa ba tare da kowa ya sani ba

Sokoto - Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu, ya kai ziyarar ba zata babban Asibiti na musamman a cikin garin Sokoto domin gane wa idonsa yadda ake duba marasa lafiya.

Rahoton Vanguard ya ce mai magana da yawun gwamnan, Malam Abubakar Bawa, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 19 ga watan Yuni, 2023.

Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sakkwato.
Gwamna Aliyu Ya Yi Badda Kama, Ya Shiga Keke Napep Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibiti Hoto: Dr. Shadi Sabe/Facebook
Asali: Facebook

Bawa ya ce mai girma gwamna ya yanke kai wannan ziyara ne bayan korafe-korafe sun cika masa tebur daga mutanen jihar kan rashin ingancin aiki a Asibitin.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Faɗi Babban Jigon da Alamu Suka Nuna Zai Koma APC, Ya Roƙe Shi Alfarma 1

Kakakin gwamnan ya ce daga cikin muhimman dalilin da suka tilastawa mai girma gwamna zuwa da kansa sun ƙunshi lalacewar mahalli, rashin wutar lantarki da lalacewar kayan aikin da na gwaje-gwaje.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ƙara da cewa gwamna Aliyu ya kai wannan ziyara ne a Keke Napep domin ya tattara bayanai masu muhimmanci daga ma'aikatan asibitin da kuma marasa lafiya.

Me gwamnan ya gano kuma wane mataki zai ɗauka?

A cikin sanarwan, Bawa ya haƙaito gwamna Aliyu na cewa:

"Na sha mamakin abinda idona ya gani yayin ziyarar awa huɗu da na kai Asibitin, naga komai da kaina. Marasa lafiya da masu jinya na cikin wani hali a mahalli mai datti kuma ga rashin kayan aikin malaman Asibiti."
"Yan uwan marasa lafiya sun koma nema wa kansu haske saboda lalacewar wutar lantarki a Asibitin. Na umarci shugabannin Asibitin su zo mu zauna mu ga yadda za'a farfaɗo da Asibitin."

Kara karanta wannan

Tsadar Man Fetur: Gwamnan Arewa Ya Samo Mafita, Za a Fara Jigilar Dalibai a Jiharsa Kyauta Ba Ko Kobo

Menene ya haddasa wannan matsala?

Wata babbar majiya a cikin masu gudanarwa na Asibitin ta shaida wa hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) cewa gwamnatin da ta gabata ce ta jawo lalacewar Asibitin.

A cewar majiyar, haka kurum tsohuwar gwamnati ta daina turo kasafin gudanar da Asibitin na wata-wata kuma hakan ya jawo komai ya zama sai Addu'a, rahoton Gazettengr ya tattaro.

Cikakken Jerin Sunaye: Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sabbin Hafsoshin Tsaron Najeriya, IGP Da NSA

A wani labarin na daban kuma Mun kawo muku cikakken jerin sunayen sabbin hafsoshin tsaron Najeriya da shugaba Tinubu ya naɗa.

A wata sanarwa da SGF ya rattaɓa wa hannu, Tinubu ya ƙara wa Nuhu Ribaɗu girma zuwa mai ba da shawara kan tsaron ƙasa (NSA).

Asali: Legit.ng

Online view pixel