Sanata Akpabio Ne Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa, Uzodinma

Sanata Akpabio Ne Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa, Uzodinma

  • Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya nuna kwarin guiwar cewa Sanata Akpabio zai samu nasarar zama shugaban majalisar dattawa
  • Ya ce kwamitin da shugaba Tinubu ya kirkira da nufin kawo karshen ruɗanin da ke tattara da tseren kujerar ya cimma nasara
  • A cewarsa Sanata Ahmad Lawan zai yi duk mai yuwuwa wajen tabbatar da nasarar Akpabio gobe Talata

Abuja - Jam'iyyar All progressives Congress (APC) mai mulkin Najeriya ta jaddada kwarin guiwar cewa ɗan takarar da take goyon baya, Sanata Godswill Akpabio, ne zai lashe zaɓen shugaban majalisar dattawa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wannan na zuwa ne ƙasa da awanni 24 gabannin rantsar da majalisar dattawa ta 10, wanda zai gudana ranar Talata, 23 ga watan Yuni, 2023.

Shugaba Tinubu, Akpabio da Gwamna Uzodinma.
Sanata Akpabio Ne Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa, Uzodinma Hoto: Buhari Sallau
Asali: Twitter

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, wanda ba'a jima ba ya zama shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, shi ne ya bayyana yakinin jam'iyyarsa yayin hira da 'yan jarida a fadar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Hotuna Da Bayanai Sun Bayyana Yayin da Tinubu Ya Karbi Bakuncin Akpabio Da Hope Uzodimma a Villa

Uzodinma ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan ganawa da shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a fadarsa Aso Rock da ke Abuja ranar Litinin, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce kwamitin da shugaba Tinubu ya kafa kuma ya ɗora masa nauyin warware ruɗanin da ke tattare da tseren neman kujerun shugabancin majalisar dattawa ya samu nasararori.

A cewar gwamnan, kwamitin ya samu ci gaba a kokarinsa na haɗa kan Sanatoci da taimakon shugaban majalisar dattawa mai barin gado, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan.

Gwamna Uzodinma ya ƙara da cewa Sanata Lawan zai yi duk mai yuwuwa domin tabbatar da ɗan takarar da jam'iyyar ke goyon baya ya zama magajinsa a majalisar dattawa.

Da yake nasa jawabin, Akpabio, tsohon gwamnan jihar Anambra kuma tsohon Minista a gwamnatin Muhammadu Buhari, ya tabbatar da cewa majalisa ta 10 karƙashin jagorancinsa zata yi aiki cikin haɗin kai.

Kara karanta wannan

Ranar Dimokuradiyya: Dalilai 5 Da Suka Sa Ranar 12 Ga Watan Yuni Ke Da Muhimmanci A Tarihin Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Rattaɓa Hannu Kan Dokar Bai Wa Dalibai Bashi

A wani rahoton na daban kuma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu kan kudirin dokar bai wa ɗaliban Najeriya bashi.

Wannan kudiri da shugaban kasa ya amince kuma ya sanya hannu zai ba ɗaliban Najeriya damar samun bashin gwamnati, wanda ba bu kuɗin ruwa a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel