Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Rattaɓa Hannu Kan Dokar Bai Wa Dalibai Bashi

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Rattaɓa Hannu Kan Dokar Bai Wa Dalibai Bashi

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya cika ɗaya daga cikin alkawurran da ya ɗauka lokacin yakin neman zabe
  • A yau Litinin, 12 ga watan Yuni, 2023, shugaban ya rattaɓa hannun kan kudirin dokar bai wa ɗalibai 'yan asalin Najeriya bashi
  • Wannan doka zata bai wa kowane ɗalibi damar karɓan bashi daga hannun gwamnati wanda ba bu kuɗin ruwa

Abuja - Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya rattaɓa hannu a kan kudirin bai wa ɗaliban Najeriya rancen kuɗi ya zama doka.

Wakilin gwamnatin tarayya, Dele Alake, ne ya bayyana haka ga manema labarai na fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja ranar Litinin da yamma.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Rattaɓa Hannu Kan Dokar Baiwa Dalibai Bashi Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Wannan kudiri da shugaban kasa ya amince kuma ya sanya hannu zai ba ɗaliban Najeriya damar samun bashin gwamnati, wanda ba bu kuɗin ruwa a ciki.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Tinubu, Gwamnan APC Ya Faɗi Sanatan da Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa

Jaridar Punch ta rahoto cewa kudirin ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilan tarayya tun a ranar 25 ga watan Mayu, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya cika alƙawurran da ya ɗauka lokacin kamfe

Da yake tsokaci kan sabon kudirin da ya zama doka yanzu, Mista Alake ya ce Tinubu ya sa hannu kan wannan doka domin cika alkawarin da ya ɗaukarwa 'yan Najeriya na sauƙaƙa musu hanyar neman ilimi.

Daily Trust ta rahoto a kalamansa yana cewa:

"Muna farin cikin sanar muku cewa yau, mintuna kaɗan da suka shige, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rattaɓa hannu kan dokar bai wa ɗalibai bashi, ku kunsan abinda wannan doka ta ƙunsa."
"Wannan alƙawari ne da mai girma shugaban kasa ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe cewa zai dawo da batun bai wa ɗaliban Najeriya bashin kuɗi kuma ga shi yau ya cika."

Kara karanta wannan

Ranar Dimokuradiyya: Dalilai 5 Da Suka Sa Ranar 12 Ga Watan Yuni Ke Da Muhimmanci A Tarihin Najeriya

"Daga yau wannan doka zata ba ɗaliban Najeriya damar samun bashi daga gwamnati domin cika burinsu na samun ilimi, haka ƙasashen duniya da suka ci gaba suke yi."

Sanata Akpabio Ne Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa, Uzodinma

A wani rahoton na daban kuma Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya nuna kwarin guiwar cewa Sanata Akpabio zai samu nasarar zama shugaban majalisar dattawa.

Wannan na zuwa ne ƙasa da awanni 24 gabannin rantsar da majalisar dattawa ta 10, wanda zai gudana ranar Talata, 23 ga watan Yuni, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel