Majalisa Ta 10: Tsohon Minista Ya Ce Kirista Dan Kudu Ya Dace Ya Gaji Kujerar Lawan, Soki Sauran Masu Nema

Majalisa Ta 10: Tsohon Minista Ya Ce Kirista Dan Kudu Ya Dace Ya Gaji Kujerar Lawan, Soki Sauran Masu Nema

  • Tsohon minista a Najeriya, Edwin Clark ya bayyana cewa ya kamata a zabi Kirista a matsayin shugaban majalisar dattawa
  • Clark ya ce lokaci ya yi da majalisar za ta hada kanta ta zabi shugaban majalisa daga Kudanci don samun daidaito a kasar
  • Jam’iyyar APC ta zabi Godswill Akpabio a matsayin wanda zai gaji shugabancin Majalisar Dattawa ta 10 da za a kaddamar

FCT, Abuja - Tsohon minista kuma shugaban hadin kan Naija Delta (PANDEF), ya ce ya kamata a zabi Kirista daga Kudancin Najeriya a matsayin shugaban majalisar dattawa ta 10.

Jam’iyyar APC ta zabi Godswill Akpabio a matsayin wanda zai gaji kujerar majalisar, amma ana samun matsaloli daban-daban daga ‘yan majalisar masu neman kujerar.

Clark ya goyi bayan Kirista dan kudanci
Tsohon Minista a Najeriya, Edwin Clark. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Da yake mai da martani akan matsalar, Edwin Clark ya ce ya kamata Majalisar Tarayyar ta yi aiki tare don ganin ta kawo yarda a tsakanin ‘yan kasa, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Kungiyar Kiristoci Ta Goyi Bayan Tsohon Gwamnan Arewa, Ta Bayyana Dalilai

Clark ya goyi bayan Kirista dan Kudanci don zama shugaban majalisar

A cewarsa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Aikin su ne a matsayinsu na masu kirkirar doka su samar da hadin kai inda ‘yan kasa za su samu aminci da kuma yarda da juna don su ji cewa su ‘yan uwan juna ne.
“Lokaci ya yi da ya kamata mu gyara kasarmu, a kokarin yin haka, muna tsammanin majalisar za su zabi Kirista daga Kudancin Najeriya a matsayin shugaba.

Clark ya caccaki El-Rufai kan kalamansa na tikitin Musulmi da Musulmi

Clark har ila yau, ya caccaki Nasir El-Rufai inda ya ce APC ta yi amfani da addini wurin cin zaben da aka gudanar na shugaban kasa, cewar rahotanni.

Ya kara da cewa::

“Magana yasasshiya ta girman kai wadda ba ta kamata ba da El-Rufai ya yi na cewa za su daura Musulmi a mulkin kasar nan har tsawon shekaru 20 har yanzu ta na sa kawo matsala a kasar.

Kara karanta wannan

Shugabancin Majalisa: Wasu ‘Yan G7 Sun Ki Zuwa Taron da Bola Tinubu Ya Kira

Majalisa Ta 10: Mambobi 67 Na Bayan Yari, Abdul Ningi Ya Bukaci a Bar ’Yan Majalisa Su Zabi Son Ransu

A wani labarin, Sanata Abdul Ningi daga jihar Bauchi ya ce akalla mambobi 67 ne ke bayan Abdulaziz Yari.

Ningi ya bayyana haka ne yayin ganawa da 'yan jaridu inda ya ce lokaci ya yi da za a barsu su zabi son ransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel