Rigima Ta Barke Wajen Zaben Kakakin Majalisa a Jihar Benue

Rigima Ta Barke Wajen Zaben Kakakin Majalisa a Jihar Benue

  • Zaɓen kakakin majalisar dokokin jihar Benue ya haifar da hatsaniya a tsakanin ƴan majalisar bayan an rantsar da su
  • Ƴan takara biyu ne dai ke neman kujerar shugabancin majalisae waɗanda suka fito daga yanki ɗaya na jihar
  • Rigimar ta kacame ne bayan wasu ƴan majalisar sun yi zargin wasu na ƙoƙarin sauya ra'ayin ƴan majalisar su zaɓi wani daban

Jihar Benue - An samu hargitsi a majalisar dokokin jihar Benue, yayin da ƴan majalisar suka riƙa musayar kalamai wajen zaɓen kakakin majalisa, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Zaman majalisar ya fara ne lokacin da gwamnan jihar Hyacinth Alia, ya rantsar da majalisar ta 10, wanda hakan ya sanya mambobinta 32 suka fara zaɓen kakakin majalisa da mataimakinsa.

Rikici ya barke kan kakakin majalisar dokokin jihar Benue
'Yan majalisar sun yi hatsaniya a tsakaninsu Hoto: Nairaland.com
Asali: UGC

Kujerar kakakin majalisar an tsara za ta fito ne daga ƙaramar hukumar Gboko a yankin Benue ta Yamma. Gwamnan ya fito ne daga yankin Benue ta Arewa maso Gabas sannan mataimakinsa ya fito daga yankin Benue ta Kudu.

Ƴan takara biyu masu neman kujerar kakakin majalisar sune Becky Orpine mai wakiltar Gboko ta Gabas da Aondonna Hyacinth Dajo, ɗan majalisa mai wakiltar Gboko ta Yamma.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Orpine ta samu goyon bayan ƴan tsagin tsohon gwamnan jihar George Akume, yayin da Dajo ya samu goyon bayan tsagin gwamnan jihar, Hyacinth Alia.

Bayan an yi zaɓen farko, dukkanin ƴan takarar sun samu ƙuri'u 16 kowanen su. Hakan ya sanya magatakardan majalisar ya ce za a sake zaɓe.

Hatsaniya ta ɓarke kan zaɓen kakakin majalisa

Majalisar ta tafi hutun minti 10 kafin dawowa domin ci gaba da zaɓen kakakin majalisa, wanda hakan ya ba ƴan majalisar damar tattaunawa da juna kan wanda yakamata a zaɓa a kujerar.

Sai dai, ana dawowa domin yin zaɓen a karo na biyu, sai hatsaniya da cece-kuce ya ɓarke a tsakanin ƴan majalisar bisa zargin cewa wasu ƴan majalisar na ƙoƙarin jan ra'ayin sauran mambobin su kada ƙuri'unsu ga wani ɗan takara.

An kwashe mintuna ƴan majalisa na tsagin Akume da tsagin Alia dake goyon bayan ƴan takarar su masu neman kujerar kakakin, suna ta hayagaga inda suka nemi da a soke zaɓen bisa zargin yin ba daidai ba a cikinsa.

Buhari Ya Yi Fatali Da Kudirin Yari Na Zama Shugaban Majalisa

A wani labarin na daban kuma, tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ƙi amincewa ya goyawa Sanata Abdulaziz Yari, baya kan neman shugabancin majalisar dattawa.

Buhari ya ce.bai kamata ya nemi kujerar ba tun da jam'iyya ta fitar da ƴan takararta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel