Kotu Ta Kori Iyorchia Ayu Daga Matsayin Shugaban Jam'iyyar PDP Na Kasa

Kotu Ta Kori Iyorchia Ayu Daga Matsayin Shugaban Jam'iyyar PDP Na Kasa

  • Wata babbar kotun jihar Benue ta cire Iyorchia Ayu, a matsayin shugaban jami'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na ƙasa
  • Babbar kotun ta soke zaman Ayu a matsayin ɗan jam'iyyar PDP, wanda hakan ya kawo ƙarshen damarsa ta komawa kan muƙaminsa
  • Kotun ta yi hukunci cewa Ayu wanda aka dakatar daga muƙaminsa, ya kasa biyan kuɗin jam'iyya wanda hakan ya sanya aka cire shi

Makurdi, jihar Benue - Babbar kotun jihar Benue mai zamanta a birnin Makurdi, ta kori Iyorchia Ayu daga matsayin shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), na ƙasa.

Mai shari'a Maurice Ikpambese, a ranar Juma'a, 2 ga watan Yuni ya kori Ayu daga jam'iyyar wanda hakan ya kawo ƙarshen fatan da ya ke da shi na komawa kan muƙaminsa na shugabancin jam'iyyar, cewar rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Ta Fasu: Muhimman Abubuwan da Su Wike Suka Tattauna da Shugaba Tinubu a Aso Rock Sun Bayyana

Kotu ta kori Ayu daga jam'iyyar PDP
Kotu ta kori Ayu daga shugancin jam'iyyar PDP Hoto: PDP, Gov Nyesom Wike
Asali: Facebook

Kafin hukuncin kotun, mai shari'a W. I Kpochi na babbar kotun jihar Benue, ya bayar da umarnin dakatar da Ayu daga kan nuna kan shi a matsayin shugaban jam'iyyar PPD na ƙasa.

Alƙalin ya bayar da wannan umarnin ne bayan wani mamban jam'iyyar a jihar Benue, Terhide Utan, ya shigar da ƙorafi a gabanta. Haka kuma shugabannin jam'iyyar PDP na mazaɓar Gyrorov a jihar sun dakatar da shi daga jam'iyyar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda Iyorchia Ayu ya yi rashin nasara

A cikin ƙarar, mai shari'a Ikpambese ya yi fatali da ƙorafin Ayu sannan ya yanke hukuncinsa.

Ya yi nuni da sashi na 8(9) na kundin tsarin mulkin PDP, inda ya ce Ayu ya daina zama ɗan jam'iyyar PDP saboda ya kasa biyan kuɗin zama ɗan jam'iyya.

Alƙalin ya kuma yi nuni da sashi na 46(1) na kundin tsarin mulkin jam'iyyar PDP, inda ya yi watsi da ƙorafin Ayu na cewa shugabannin jam'iyya a matakin mazaɓa, ba za su iya hukunta mamba na kwamitin gudanarwar jam'iyyar na ƙasa ba.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Najeriya Sun Ziyarci Tsohon Shugaba Buhari a Daura, Hotuna Da Bayanai Sun Fito

Matsalolin Ayu dai sun ƙara yawa ne lokacin da mambobin jam'iyyar PDP na mazaɓarsa suka dakatar da shi a watan Maris, jim kaɗan bayan Atiku Abubakar ya faɗi zaɓen shugaban ƙasa.

Daga ƙarshe, dai hukuncin babbar kotun ya tabbatar da cire Ayu a matsayin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, rahoton Tribune ya tabbatar.

Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan PDP

A wani rahoton na daban kuma, kotu ta yi hukuncin kan ƙarar da ke ƙalubalantar nasarar gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde.

Kotun ta kori ƙarar da jam'iyyar AA ta shigar tana ƙalubalantar nasarar gwamn Makinde a zaɓen gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel