Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan PDP

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan PDP

  • An kori ƙarar neman soke nasarar Gwamna Seyi Makinde na PDP a zaɓen gwamnan jihar Oyo na 2023 da ya gabata
  • Kwamitin mutum uku ƙarƙashin jagorancin Ejiron Emudainohwo ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a, 2 ga watan Yuni
  • Kafin hukuncin da kotun ta yanke, lauyan wanda ya shigar da ƙara ya nemi da a dakatar da shari’ar, amma sai aka yi watsi da roƙon nasa

Oyo, Ibadan – Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta jihar Oyo ta tabbatar da nasarar Gwamna Seyi Makinde a zaɓen gwamnan jihar Oyo na 2023 da ya gabata.

Idan ba a manta ba, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ayyana Gwamna Makinde a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar ta Oyo.

Kotu ta tabbatar da nasarar Seyi Makinde
Kotu tayi watsi da karar da ke kalubalantar nasar Seyi Makinde. Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Makinde dai ya samu ƙuri’u 563,756 inda kuma ya samu nasara a ƙananan hukumomi 31 daga cikin 33 na jihar.

Kara karanta wannan

Ta Fasu: Muhimman Abubuwan da Su Wike Suka Tattauna da Shugaba Tinubu a Aso Rock Sun Bayyana

Babban abokin hamayyar Gwamna Makinde, ɗan takarar jam’iyyar APC, Teslim Folarin kuma ya samu ƙuri’u 256,685 inda ya zo na biyu a zaɓen, a yayin da ɗan takarar Accord Party, Adebayo Adelabu ya samu ƙuri’u 38,357 kuma ya zo na uku.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai ɗan takarar jam’iyyar AA, Babatunde Ajala, bai gamsu da sakamakon zaɓen ba, wanda hakan ya sanya shi kai ƙarar Gwamna Makinde yana mai neman a soke zaɓen nasa.

Ana ƙarar Makinde, INEC da PDP

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, bayan gwamnan da yake ƙara, Ajala ya kuma bayyana sunayen INEC da PDP a cikin karar da ya shigar gaban kotu.

Sai dai kwamitin mutane uku da Ejiron Emudainohwo ya jagoranta, ya yi fatali da ƙarar da Ajala ya shigar a kan duka kararakin uku.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Najeriya Sun Ziyarci Tsohon Shugaba Buhari a Daura, Hotuna Da Bayanai Sun Fito

Jaridar Vanguard kuma ta ruwaito cewa, kotun ta kuma ci ɗan takarar na AA, tarar N600,000, inda za a bai wa INEC N100,000 sannan kuma N250,000 ga Gwamna Makinde da PDP kowanensu.

Lauyan mai ƙara ya roƙi a dakatar da shari'ar

Kafin yanke hukuncin, lauyan wanda ya shigar da ƙara, Etibo Orowo King, ya roƙi kotun da ta dakatar da shari'ar.

A cewarsa:

“Roƙona shi ne a soke sakamakon zaɓen. Amma, bayan sake nazari, mun yanke shawarar dakatar da shari’ar domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.”

A martanin da ya mayar kan mai shigar da ƙarar, lauyan Gwamna Makinde da PDP ya buƙaci kotun da ta yi watsi da karar ta su.

A kalamansa:

“Mai shigar da ƙara ya nemi a dakatar shari’ar. Muna roƙon a yi watsi da ƙarar. Koke ne dama da yake korarre tun lokacin da aka shigar da shi.”

Kara karanta wannan

Abin Da Buhari Ya Gaza Yi A Shekarunsa 8 Kan Mulki, Mataimakin Shugaban APC Ya Yi Bayani

Tinubu ya naɗa muƙamai a makonsa na farko a kan karaga

A wani labari da Legit.ng ta wallafa a baya, kun ji cewa Shugaba Tinubu ya sanar da naɗa sabbin muƙamai a makonsa na farko a kan karagar mulki.

An dai rantsar da sabon shugaban ƙasar ne a ranar 29 ga watan Mayu, a babban birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel