Gwamnonin Najeriya Sun Ziyarci Buhari a Daura, Bayanai Sun Fito

Gwamnonin Najeriya Sun Ziyarci Buhari a Daura, Bayanai Sun Fito

  • Gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC da wasu jam'iyyun sun ziyarci tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari
  • Tsohon kakakin shugaban ƙasa, Garba Shehu, shine ya tabbatar da hakan a wani rubuta da ya yi a Twitter tare da hotuna
  • A ranar Litinin 29 ga watan Mayu, Buhari ya miƙa mulki a hannun Tinubu inda ya koma Daura domin ci gaba da rayuwarsa a can

Jihar Ƙatsina - Kwanaki kaɗan bayan ya miƙa mulkin Najeriya a hannun shugaban ƙasa Bola Tinubu, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya karɓi baƙuncin gwamnonin Najeriya a gidansa da ke Daura.

Tsohon kakakin shugaban ƙasa, Garba Shehu, shine ya bayyana hakan a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter, ranar Alhamis, 1 ga wata Yuni 2023.

Gwamnonin Najeriya sun ziyarci Buhari
Tsohon shugaba Muhammadu Buhari tare da gwamnonin a Daura Hoto: @GarShehu
Asali: Twitter

Dalilin da ya sanya gwamnonin suka ziyarci Buhari

A cewar Garba Shehu, gwamnonin sun ziyarci tsohon shugaban ƙasar ne domin nuna godiyar su kan yadda ya sadaukar da kansa wajen mulkin ƙasar nan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tun bayan da Buhari ya koma Daura, ya riƙa samun ziyarar manyan mutane daga sassa daban-daban na ƙasar nan waɗanda ke zuwa domin taya shi murnar yadda ya kammala mulkinsa lafiya.

Da ya ke jawabinsa a wajen ganawa da gwamnonin, Buhari ya nuna godiyarsa bisa ƙaunar da suka nuna masa a shekara takwas da suka gabata, inda ya ce yana tunanin da wuya a samu tsohon shugaban da aka nunawa irin wannan ƙaunar.

Gwamnonin da suka kai ziyarar sun haɗa da gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, wanda ya wakilci shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya, gwamna Abdulrahman AbdulRazak, shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.

Sauran sun haɗa da shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya, gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, gwamnan Katsina Dikko Umar Radda, gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, gwamnan Legas, Babajide Sanwo-olu da gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule.

Jigon APC Ya Bayyana Abinda Buhari Ya Gaza a Shekara 8

A wani rahoton na daban kuma, mataimakin jam'iyyar APC na ƙasa ya bayyana ta fuskar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ta gaza a shekara takwas yana mulki.

Salihu Lukman ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta gaza ɗaukar matakan ƙalubalen abinda ya addabi ƙasa a okacin mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel