“Lokaci Bai Yi Ba”: Ayodele Ya Ce Cire Tallafin Man Fetur Zai Bata Gwamnatin Tinubu

“Lokaci Bai Yi Ba”: Ayodele Ya Ce Cire Tallafin Man Fetur Zai Bata Gwamnatin Tinubu

  • Primate Elijah Ayodele ya nuna rashin amincewa da cire tallafi mai da shugaban kasa Tinubu ya yi, yana mai gargadin cewa zai yi wa gwamnatin illa da kai ga mawuyacin tattalin arziki
  • Malamin addinin ya ce sai wani ikon Allah ne kadai zai kawo sauyi mai kyau sannan ya gargadi yan Najeriya da kada su yi tsammanin samun gagarumin ci gaba daga gwamnatin Tinubu
  • Ayodele ya kuma yi hasashen diramomin siyasa, karairayi da matsaloli wajen yaki da rashawa, inda ya bukaci yan kasa da su yi hakuri da addu'a

Lagos - Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, ya nuna rashin yarda da matakin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na cire tallafin man fetur.

A wata sanarwa da hadimin labaransa, Osho Oluwatosin ya saki, Primate Ayodele ya nanata cewa ya yi wuri da Tinubu zai soke tallafin mai, domin hakan zai yi illa ga gwamnatinsa, Daily Independent ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Gaske Dan Shugaban INEC Ya “Haukace” a Saudiyya? Gaskiya Ta Bayyana

Shugaban kasa Bola Tinubu da Primate Ayodele
“Lokaci Bai Yi Ba”: Ayodele Ya Ce Cire Tallafin Man Fetur Zai Bata Gwamnatin Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Primate Babatunde Elijah Ayodele
Asali: Twitter

Ikon Allah ne kawai zai kawo sauyi mai kyau, Inji Primate Ayodele

Malamin addinin ya yi hasashen mawuyacin tattalin arziki da wahalar da rahamar Ubangiji ne kawai zai iya daidaita abubuwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Primate Ayodele ya bayyana cewa yanayin rikon da shugaban kasar ke yi wa lamarin tallafin mai bai dace ba, sannan ya gargadi yan Najeriya da kada su yi tsammanin abubuwa da dama daga gwamnatin yanzu.

"Duk yadda kake son sa shi, lokaci bai yi ba da za a cire tallafin man fetur, zai lalata gwamnati mai ci. Ya kamata su yi aiki kan tallafin mai da fasaha.
"Babu yadda za a yi abubuwa ba za su yi wahala ba, babu yadda za a yi ba za mu fuskanci matsin tattalin arziki ba. Tinubu ba zai inganta wannan gwamnati ba har zuwa 2026 idan ba Allah ya so kawo sauyi ba.

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Yi Wa APC Wankin Babban Bargo a Kaduna, Ya Bayyana Wani Bangare Na Musamman Da Jami'yyar Ta Gaza

"Babu aibu tattare da cire tallafin mai amma tsarin cire shi din ne yake haddasa matsaloli a yanzu.
"Magana ta gaskiya, Tinubu bai magance lamarin da kyau ba. Kada yan Najeriya su yi tsammanin abubuwa da yawa daga Tinubu cikin shekaru hudunsa na farko a mulki."

Diramar siyasa da karairayi a gwamnatin Tinubu

Primate Ayodele ya kuma yi gargadin cewa za a tafka wasan kwaikwayo na siyasa da yaudara a cikin sabuwar gwamnatin.

A cewar malamin addinin, jami'an gwamnati za su yanke shawarar fadin karairayi, haddasa firgici da rashin yarda tsakanin al'umma.

Tinubu zai yi kokarin yaki da rashawa, Inji Ayodele

Primate Ayodele ya ci gaba da bayanin cewa koda dai Tinubu zai yi kokarin yaki da rashawa, zai fuskanci gagarumin turjiya da zai kawo tsaiko ga kokarin gwamnatinsa.

Malamin addinin ya yarda cewa Ubangiji na nufin amfani da gwamnatin Tinubu don koyawa yan Najeriya darasi, don koyar da su yadda za su girmama shi da kuma godewa kasancewarsa a duk al’amuransu.

Kara karanta wannan

“Sai An Tauna Tsakuwa Idan Za a Kai Najeriya Gaba”: Wike Ya Goyi Bayan Tinubu Kan Cire Tallafin Mai

Ayodele ya bukaci al'umma da su yi hakuri sannan su yawaita addu'a, yana mai cewa akwai babban aiki ja a gaba.

Legit.ng ta nemi jin ta bakin wasu yan Najeriya don jin yadda lamarin cire tallafin mai ya taba su.

Mallam Abu mai sana’ar tuka adaidaita sahu ya ce:

“Babu abu da za mu ce da wannan al’amari sai innalillahi wa’inna illaihi raji’un. Ya ake so mu yi da ranmu. Ka siya litar mai N540 ka ce wa fasinja ga kudin da zai biya na daukarsa ya ce sam ba haka ba.
“Har dama masu sabuwar keke, amma mu masu tsohuwar keke wahala za mu sha domin shan mai ne da ita. Don Allah gwamnati ta duba wannan al’amari ta kawo mana agaji don kada mu rasa hanyar cin abincinmu.

Malama Asiya kuwa cewa ta yi:

“Ya talaka zai yi? Na hau keke daga nan city gate na Minna zuwa nan UK bello mai adaidaita ya je sai dai na biya N150 abun da muke biyan N70 idan ya yi yawa kenan. Kuma bai da laifi idan ba haka ba ta ina zai fita a sana’ar tasa. Don Allah a kawo mana dauki a kasar nan.”

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Kara Mafi Karancin Albashi? Shugaban Kasa Ya Yi Sabuwar Sanarwa

Wike ya goyi bayan Tinubu kan cire tallafin man fetur

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya goyi bayan cire tallafin man fetur da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi.

Wike ya ce dole sai an tauna tsakuwa idan har ana son a ciyar da kasar Najeriya gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel