Shehu Sani Ya Caccaki Gwamnatin Jam'iyyar APC a Jihar Kaduna

Shehu Sani Ya Caccaki Gwamnatin Jam'iyyar APC a Jihar Kaduna

  • Shehu Sani ya yi wa jam'iyyar APC wankin babban bargo a Kaduna inda ya zargeta da rashin iya gudanar da mulki
  • Tsohon sanatan na Kaduna ta tsakiya ya kuma abokan adawarsa na siyasa da jifarsa da sharri domin ganin bayansa
  • Shehu Sani ya gargaɗi Tinubu dangane da yin aiki da El-Rufai a gwamnatinsa inda ya ce tsohon gwamnan bai cancanci samun muƙami ba

Abuja - Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya caccaki gwamnatin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar Kaduna, inda ya zarge su da rashin iya gudanar da mulki, cewar rahoton Vanguard.

Da ya ke tattaunawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja, Shehu Sani ya nuna ɓacin ransa kan halin da jihar ta ke ciki, inda ya yi nuni kan irin jifarsa da abokan adawarsa ke yi, sannan ya sha alwashin gayawa gwamnati gaskiya duk kuwa abinda hakan zai janyo.

Kara karanta wannan

Iyaye Sun Bayyana Yadda Wasu ’Yan Banga Suka Lakadawa Dansu Duka Har Lahira a Kano

Shehu Sani ya caccaki mulkin APC a Kaduna
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, sanata Shehu Sani Hoto: Leadership.com
Asali: UGC

A kalamansa:

"Ƴan bindiga sun farmaki ofishina sannan ƴan daba na bin sahu na duk inda na je. Sun kuma umarci sojoji su cafke ɗaya daga cikin hadimai na Bashir Ahmad a shekarar 2017."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sojoji sun azabtar da Bashir domin ya yi min ƙazafi a wani laifin kisan kai da bani da masaniya a kai. Ƴan sanda sun yi watsi da shi bayan sun gano cewa ƙagen siyasa ne."

Tsohon sanatan ya yi wa El-Rufai wankin babban bargo

Sani ya kuma yi kalamai masu tsauri kan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, inda ya zarge shi da barin jihar cikin ɗumbin bashi, kashe-kashe da sace-sacen mutane, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

A cewar tsohon sanatan, shekara takwas na mulkin El-Rufai cike su ke da baƙin ciki da kama karya, inda tsohon gwamnan ya riƙa nuna wariya ga al'ummar yankin Kudancin Kaduna.

Kara karanta wannan

"Ka Fuskancemu Mu Yaransa Don Mune Sa'anninka, Dan El-Rufai Ya Yi Wa Shehu Sani Wankin Babban Bargo

Shehu Sani ya gargaɗi shugaba Bola Tinubu, da ya yi takatsantsan kada ya saki jiki da El-Rufai.

"Elrufai ya marawa Amaechi baya a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa. Sannan lokacin zaɓen shugaban ƙasa ya mayar da hankali ne kawai ɗansa ya ci zaɓen ɗan majalisar tarayya, inda ƴa bari Tinubu ya rasa Kaduna a hannun Atiku. Babban haɗari ne El-Rufai ya shiga cikin gwamnatin Tinubu." A cewarsa.

Shehu Sani Ya Tona Asirin El-Rufai

A wani labarin na daban kuma, tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai na jiran samun muƙami a gwamnatin Tinubu.

Shehu Sani ya ce gwamnan ya ci dunduniyar shugaba Tinubu, inda ya shawarci shugaban ƙasar da ya yi hankali da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel