Tinubu Ya Yi Tsokaci Kan Karin Mafi Karancin Albashi, Ya Bakaci Gwamnonin APC Su Yi Aiki Tare

Tinubu Ya Yi Tsokaci Kan Karin Mafi Karancin Albashi, Ya Bakaci Gwamnonin APC Su Yi Aiki Tare

  • Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ce yana so a sake duba lamarin mafi karancin albashi a Najeriya
  • Ya bayyana cewa akwai bukatar sake duba mafi karancin albashin yanzu don ya yi daidai da yanayin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki a yanzu
  • Shugaban kasar ya ba da sanarwar nan ne a ranar Juma'a, 2 ga watan Yuni yayin wata ganawa da gwamnonin APC a fadar shugaban kasa Abuja

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa akwai bukatar kara mafi karancin albashin kasar domin inganta yanayin rayuwar al'ummar Najeriya.

Tinubu ya yi wannan kiran ne a ranar Juma'a, 2 ga watan Yuni yayin ganawarsa da gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Bola Tinubu da gwamnonin APC
Tinubu Ya Yi Tsokaci Kan Karin Mafi Karancin Albashi, Ya Bakaci Gwamnonin APC Su Yi Aiki Tare Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Ya bayyana cewar ya zama dole a sake duba mafi karancin albashi domin ya yi daidai da halin da yan Najeriya ke ciki a yanzu, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aikin Gama Gari, Ta Ba Gwamnatin Tinubu Sabon Wa’adi

Shugaban kasa Tinubu ya bukaci dukkanin gwamnonin APC da su yi aiki tare sannan su ba lamarin fifiko don ganin mafarkinsa ya zama gaskiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Muna bukatar yin wasu yan lisaffe-lissafe da bincike kan karancin albashi," inda ya kara da cewar, "ya zama dole mu duba lamarin tare, da kudaden shigar. Dole mu karfafa tushen da amfani da kudaden shigarmu."

Shugaban kasa Tinubu ya bukaci gwamnonin da su riki yarda da amincin da wadanda suka zabe su da dubban yan Najeriya suka yi masu ta hanyar kawo sauyi don inganta rayuwar yan Najeriya.

"Wannan taron ba bakon abu bane a gareni, kuma abubuwan da taron ya kunsa suna da muhimmanci sosai. Kawancen akwai ban sha'awa sosai. Wannan kan aikin Najeriya ne ba wai Bola Tinubu ba."

Dangane da batun hauhawar farashin kayayyaki, Shugaban kasa Tinubu ya ce akwai bukatar a daidaita shi.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Fara Mulki da Ciwon Kai, ‘Yan Kwadago Sun Sa Ranar Shiga Yajin-Aiki

Kungiyar kwadago ta yi barazanar shiga yajin aikin gama gari

A wani labarin, kungiyar kwadago ta kasa ta yi barazanar shiga yajin aiki daga ranar Laraba, 7 ga watan Yuni a kan cire tallafin man fetur.

Kungiyar ta NLC ta nemi gwamnatin tarayya musamman NNPC da ta mayar da farashin man fetur yadda yaka a baya kafin wannan rana ko kuma su fara zanga-zangar sai baba ta gani.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel