Ka Fuskance Ni Don Mahaifina Ba Sa’anka Bane, Dan El-Rufai Ya Caccaki Shehu Sani

Ka Fuskance Ni Don Mahaifina Ba Sa’anka Bane, Dan El-Rufai Ya Caccaki Shehu Sani

  • Rikici tsakanin tsohon sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya dauki sabon salo
  • Bashir, dan tsohon gwamnan Kaduna ya gargadi Sanata Sani a kan ya daina caccakar mahaifinsu don ba sa'ansa bane
  • A cewar dan tsohon gwamnan, su 'ya'yansa sune abokan yin Shehu Sani kuma daidai suke da shi

Bashir, dan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya yi Allah wadai da tsohon sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, kan shaguben da ya yi wa mahaifinsa game da bayyana kadarorinsa na 2015 da 2023.

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, Sani ya zargi El-Rufai da barwa jihar Kaduna tarin bashi, duk da ikirarin da ya yi cewa bai taba wawure kudaden jihar ba.

Shehu Sani, Nasir El-rufa da Bashir El-rufai
Ka Fuskance Ni Don Mahaifina Ba Sa’anka Bane, Dan El-Rufai Ya Caccaki Shehu Sani Hoto: Naija News
Asali: UGC

Shehu Sani ya kalubalanci El-Rufai ya bayyana fom din kadarorinsa na 2015 da 2023

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Yi Wa El-Rufai Tonon Silili, Ya Bayyana Abinda Ya Ke Jiran Samu Daga Wajen Shugaba Tinubu

Ya yi zargin cewa tsohon gwamnan na jiran shugaban kasa Bola Tinubu ya ba shi mukamin siyasa bayan ya gama yi wa Rotimi Amaechi aiki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sani ya kuma kalubalanci El-Rufai da ya wallafa fom din kadarorinsa ya gabatarwa hukumar kula da da'ar ma'aikata a 2015 da 2023.

"Mista Elrufai, tsohon gwamna mai ritaya ya koma watsa labarai a Twitter, yayin da ya ke jiran mukami daga wajen Tinubu, bayan ya yi wa Amaechi aiki da yada labarai marasa kyau ta karkashin kasa.

"Ka bar tarin bashi ga yayanmu da jikokinmu su biya a jihar Kaduna, sannan ka yi ikirarin ba ka taba satar ko sisi daga asusun jihar Kaduna ba. Daya daga cikin yan barandarka har cewa ya yi arzikin ka ma raguwa ya yi.
"Idan ka isa ka bayyana kadarorin ka ta hanyar nunawa duniya fom din da miƙawa hukumar da'ar ma'aikata, daga na shekarar 2015 har na 2023. Zan yi maka martani idan ka yi hakan."

Kara karanta wannan

Ba a Ba Ni Mukamin Komai ba Inji Wanda Ake Cewa Ya Zama Kakakin Shugaban Kasa

Mahaifinmu ba sa'anka bane, Bashir El-rufai ya yi martani ga Shehu Sani

Da yake martani ga wallafarsa, Bashir ya bukaci Sani da ya tsayar da rikicin Twitter a tsakanin mutanen da suke sa'anninsa sannan kada ya kai abun kan mahaifinsa.

Bashir ya wallafa a a shafinsa:

"Da gaske haka kake magana da manyanka? Ka dakatar da wannan rikici na Twitter tsakaninka da mu, yaransa. Mune sa'anninka."

Gwamna Uzodimma ya zama shugaban gwamnonin APC

A wani labari na daban, mun ji cewa gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ya zama shugaban kungiyar gwamnonin APC.

Hakan ya kasance ne bayan gwamnan ya yi nasara a zaben kungiyar da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, 31 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel