INEC Ta Bayyana Sahihin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kaduna a Kotu

INEC Ta Bayyana Sahihin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kaduna a Kotu

  • Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta faɗa wa Kotun sauraron ƙarar zabe cewa Uba Sani na jam'iyyar APC ne ya ci zaben gwamnan Kaduna
  • Hukumar ta bayyana wa Kotun cewa zaben gwamnan da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris, 2023 a Kaduna sahihi ne
  • INEC ta yi wannan bayani ne yayin martani kan karar da PDP da ɗan takararta, Isa Ashiru Kudan suka shigar suna kalubalantar nasarar Uba Sani

Kaduna - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce ɗan takara a inuwar APC, Malam Uba Sani, ne ya samu nasarar lashe zaɓen gwamna a Kaduna.

INEC ta bayyana haka ne yayin da Kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan Kaduna ta nemi karin haske kan korafe-korafen da PDP ta shigar game da zaben ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Malam Uba Sani.
INEC Ta Bayyana Sahihin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kaduna a Kotu Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Facebook

PDP da ɗan takararta na gwamna sun garzaya Kotun inda suka kalubalanci nasarar Malam Uba Sani, a cewarsu an tafka kura-kurai a sakamakon zaɓen.

Uba Sani ne ya ci zaɓe - INEC

Da take martani dangane da ƙarar, INEC ta ce sabon gwamna Uba Sani ne sahihin wanda ya ci zaɓen da ya gabata kamar yadda doka ta tanada, rahoton Tribune ya tabbatar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Vanguard ta tattaro cewa martanin INEC na kunshe ne a bayanin da hukumar ta yi na farko kan ƙarar jam'iyyar PDP da ɗan takararta na gwamnan Kaduna.

Sabon gwamnan Ƙaduna ya fara ɗaukar matakai kan tsaro

A halin yanzu, sabon gwamnan Kaduna da ya karbi shahadar kama aiki, Malam Uba Sani, ya ɗauki muhimmin alkawari a wurin taron majalisar tsaron jihar.

Gwamnan ya sha alwashin samar da dukkan kayan aikin da hukumomin tsaro ke buƙata domin kawo karshen matsalar tsaron da ta dabaibaiye jihar Kaduna.

Ya jaddada cewa kwanciyar hankali da tsaro na sahun gaba a cikin jerin kudirori 7 da gwamnatinsa ta sa a gaba.

Gwamnonin PGF Sun Ɗauki Matsaya Kan Batun Cire Tallafin Man Fetur a Najeriya

A wani rahoton na daban kuma Gwamnonin APC sun gana da shugaban ƙasa, sun ɗauki matsaya kan batun cire tallafin man fetur a Najeriya.

Sai dai gwamnonin sun bayyana takaicinsu bisa tashin farashin litar mai farat ɗaya biyo bayan kalaman shugaban kasa a wurin bikin rantsuwar kama aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel