A Karshe INEC Ta Bayyana Ainihin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kaduna

A Karshe INEC Ta Bayyana Ainihin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kaduna

  • An bayyana ainihin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kaduna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris
  • Hukumar zabe na kasar, INEC, a baya-bayan nan ta fada wa kotun zabe cewa Uba Sani, dan takarar gwamnan APC a Kaduna ya lashe zaben, tana mai cewa zaben adalci da gaskiya aka yi
  • INEC ta bukaci kotun ta lura da wani babban kuskure da ya ci karo da kundin tsarin mulkin kasa a cikin karar da PDP ta yi na kallubalantar sakamakon zaben na ranar 18 ga watan Maris

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Kasa, INEC, ta sanar da ainihin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kaduna.

Hukumar shirya zabe na kasar, INEC, ta ce dan takarar jam'iyyar da ke mulkin jihar, wato All Progressives Congress, Uba Sani, shine ya lashe zaben gwamnan jihar.

INEC ta fada wa kotu Uba Sani ne ya ci zaben gwamnan Kaduna
INEC ta fada wa kotun zabe cewa Uba Sani na APC ne ya lashe zaben gwamnan jihar Kaduna na ranar 18 ga watan Maris. Hoto: Sanata Uba Sani
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Uba Sani ne ya lashe zabe, INEC ta bayyana

Hakan na zuwa ne yayin da INEC ta ankarar da kotun zaben dangane da wani babban kuskure da ya saba wa kundin tsarin mulki cikin karar da jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta yi na kallubalantar sakamakon zaben gwamnan da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.

A martaninta kan karar, INEC, ta ce gwamna mai ci yanzu kuma dan takarar jam'iyyar APC mai mulki a jihar, Uba Sani, ya lashe zaben ba tare da wani kumbiya-kumbiya ba kuma bisa tsarin doka aka ayyana shi matsayin wanda ya yi nasara, Nigerian Tribune ta rahoto.

Amsar da hukumar ta bada na cikin rahotonta na rashin amincewa da karar da PDP da dan takararta na gwamna, Mohammed Ashiru Sani suka shigar, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Sabon gwamnan na Kaduna ya yi muhimmin alkawari a taronsa na farko da shugabannin hukumomin tsaro

Sanata Uba Sani, sabon gwamnan na jihar Kaduna ya yi muhimmin alkawari a taron farko da gwamnatinsa ta yi na Majalisar Tsaro.

Gwamnan ya sha alwashin bada tallafi na zirga-zirga ga hukumomin tsaro domin taimaka musu wurin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Ya jadadda cewa samar da tsaro da zaman lafiya na daya cikin muhimman abubuwa 7 da gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali a kansu a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel