Tawagar Lauyoyina Zasu Tabbatar Zaben 2023 Damfara Ce, Atiku Ya Maida Martani

Tawagar Lauyoyina Zasu Tabbatar Zaben 2023 Damfara Ce, Atiku Ya Maida Martani

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya maida martani kan hukuncin da Kotun koli ta yanke ranar Jumu'a
  • Atiku ya ce hukuncin ba zai sa ya ja da baya ba a kokarinsa na tabbatar wa duniya zaben 2023 cike yake da damfara
  • Kotun koli ta yi watsi da ƙarar jam'iyyar PDP ta neman a soke sahihancin takarar Tinubu saboda Shettima ya nemi kujeru 2

Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya jaddada cewa tawagar lauyoyinsa zasu tabbatar da cewa zaben da aka yi damfara ce.

Atiku ya faɗi haka ne yayin martani kan hukuncin da Kotun koli ta yanke ranar Jumu'a, inda ta yi watsi da ƙarar PDP ta neman soke sahihancin takarar Kashim Shettima a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.

Atiku Abubakar.
Tawagar Lauyoyina Zasu Tabbatar Zaben 2023 Damfara Ce, Atiku Ya Maida Martani Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Depositphotos

Punch ta ce kwamitin alkalai 5 na Kotun koli ya yanke cewa jam'iyyar PDP ba ta hurumin shigar da wannan ƙara saboda ba mambar APC bace.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Ƙarar da Ta Nemi Dakatar da Rantsar da Bola Tinubu

Martanin Atiku game da hukuncin Kotun koli

Da yake martani kan wannan hukuncin, Tsohon mataimakin shugaban kasan ya kafe kan bakarsa cewa tawagar lauyoyinsa ba zasu ja da baya ba sai sun tabbatar zaben 2023 damfara ce.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A rubutun da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Atiku ya ce:

"Korar ƙarar PDP da Ƙotun koli ta yi ba zai sace mana guiwa ba a kokarin tabbatar da adalci. Tawagar lauyoyinmu zasu gamsar da duniya cewa zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023 damfara ce, ya saɓa wa kwansutushin da kundin dokar zabe."
"Haka kuma wanda aka ce ya samu nasara bai halatta ya tsaya takara ba a zaben. Yaƙin tabbatar da Demokuraɗiyya da kawo ci gaba a Najeriya muka sa a gaba kuma ba mu da shirin juya baya."
"Na san nan ba da jimawa ba gaskiya zata yi halinta, karya da fashin nasarar ɗa aka mana zasu gushe. Ina kira ga magoya bayana su kara hakuri kuma su zauna lafiya yayin da muke fafatuka a Kotun zaɓe."

Kara karanta wannan

Kotun Koli a Najeriya Ta Yanke Hukunci Kan Karar da PDP Ta Nemi a Soke Takarar Tinubu da Shettima

Bola Tinubu ya ƙara samun nasara a Kotu

A wani rahoton na daban kuma Kotu ta kori ƙarar da wasu mutum uku suka nemi a dakatar da bikin rantsar da zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu.

Babbar kotun tarayya ta yi watsi da ƙarar wasu mutum 3 da suka nemi a hana rantsar da Tinubu. Haka nan ta ci masu kara tarar miliyan N15m da wata Miliyan N5m ta daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262