Abubuwa 7 Game da Ministan Buhari da Tinubu Ya Zaba a Matsayin Sakataren Gwamnati

Abubuwa 7 Game da Ministan Buhari da Tinubu Ya Zaba a Matsayin Sakataren Gwamnati

  • Tsohon Gwamna, George Akume mai shekara 69 a Duniya zai dare kujerar Sakataren Gwamnati
  • Bola Ahmed Tinubu ya dauko kwararren ‘dan siyasar wanda tun a 2011 yake tare da shi a jam'iyyar ACN
  • Akume ya yi mulkin Jiha, ya yi Sanata a Majalisar Dattawa, sannan ya yi shekaru hudu yana Minista

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya zabi George Akume a matsayin wanda zai zama Sakataren gwamnatin tarayya, zai gaji kujerar Boss Mustapha.

Wannan rahoto ya tsakuro maku kadan daga cikin tarihin George Akume wanda ya rike matsayin Gwamnan Jiha, Sanata da kuma Minista a Najeriya.

George Akume
Buhari tare da George Akume Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wanene George Akume?

1. Haihuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanan da mu ka samu daga shafin Wikipedia ya nuna a ranar 27 ga watan Disamban 1953 aka haifi George Akume a yankin Wannune Tarka a jihar Benuwai.

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: Bankin CBN Ya Karyata Labarin Karya Darajar Naira Zuwa N630/$1

2. Makaranta

Bayan karatun firamare da sakandare, Akume ya tafi jami’ar Ibadan ya samu digirin farko a ilmin karantar halayyar ‘Dan Adam da digirgi a harkar alakar ‘yan kwadago.

3. Siyasa

A shekarar 1999 ne sabon SGF din ya yi suna a siyasa, ya zama Gwamna a jihar Benuwai, ya kafa tarihin zama mutum na farko da ya zarce a kan wannan kujera.

4. Majalisa

Bayan kammala wa’adin Gwama a 2007, Akume ya yi takarar Sanatan Arewa maso yammacin Benuwai, har ya taba zama shugaban marasa rinjaye a majalisa.

Sanatan ya nemi tazarce a karkashin jam’iyyar adawa ta ACN, kuma ya yi nasara a zaben 2011, karshensa a majalisa ya zo ne da jam’iyyar PDP ta doke shi a 2015.

5. Minista

Bayan an hana shi zarcewa a kujerar Sanata sai Muhammadu Buhari ya zabe shi ya zama Minista, aka tura shi zuwa ma’aikatar harkoki na musamman a Agustan 2019.

Kara karanta wannan

Tajuddeen Abbas Ya Fadi Adadin Magoya Bayansa a APC, PDP, LP a Zaben Majalisa

6. Tafiye-tafiye

Daily Trust ta ce Akume mutum ne mai sha’awar yawo, ya je kasashe irinsu Amurka, Ingila, Jamus, Faransa, Italiya, Kuba, Ghana, Indiya, Thailand da Jafan.

Tsohon Gwamnan ya taba zuwa Afrika ta Kudu, Jamaica, Israila, Brazil, Colombiya, Taiwan, Suwidin, Denmark, Holland, Mexico, Switzerland da sauransu.

7. Regina Akume

A zaben 2023, tsohuwar uwargidar jihar Benuwai, Regina Akume ta lashe kujerar Gboko/Tarka a majalisa, tayi takara a APC ta na mai doke John Dyegh na PDP.

Mai dakin Akume ta samu kuri’u 47,086, na biyu wanda Daily Post ta ce tsohon yaron mai gidanta ne, ya tashi da kuri’u 24,639. A watan nan za ta zama ‘yar majalisa.

Shari'ar zaben 2023

An samu labari Atiku Abubakar da jam’iyyarsa sun kafa hujja da BVAS domin nuna APC ta ci zabe ne da magudi, ta bukaci kotu ta ruguza nasarar Bola Tinubu.

Eyitayo Jegede SAN ya kawo sakamakon zaben shugaban kasa a gaban kotun sauraron karar zabe, haka zalika Peter Obi ya na da korafi game da zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel