Tajuddeen Abbas Ya Fadi Adadin Magoya Bayansa a APC, PDP, LP a Zaben Majalisa

Tajuddeen Abbas Ya Fadi Adadin Magoya Bayansa a APC, PDP, LP a Zaben Majalisa

  • Tajudeen Abbas ya ce ya samu goyon bayan mutum fiye da 200 yanzu a zaben majalisar tarayya da za ayi
  • ‘Dan takaran ya ce ‘yan jam’iyyar APC, LP, PDP da sauran jam’iyyun takwas da ke majalisa su na tare da shi
  • Hon. Abbas ya yi wannan bayani a lokacin da ya je neman goyon bayan Gwamna Ademola Adeleke a Osun

Abuja – Hon. Tajudeen Abbas ya shaida cewa mutane 200 daga cikin abokan aikinsa, sun yi masa mubaya’a ya zama shugaban majalisar wakilan tarayya.

A ranar Alhamis, The Nation ta rahoto Honarabul Tajudeen Abbas ya na mai bayanin irin goyon bayan da ya samu zuwa yanzu, a takarar da yake yi a APC.

Abbas ya jagoranci ‘yan kungiyar Joint Task da ke goyon bayan shi zuwa wajen Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke domin samun goyon bayansa.

Kara karanta wannan

Ba a Ba Ni Mukamin Komai ba Inji Wanda Ake Cewa Ya Zama Kakakin Shugaban Kasa

Tajuddeen Abbas
Tajuddeen Abbas da Ben Kalu a Osun Hoto: Rt. Hon. Tajuddeen Abbas Media Crew
Asali: Facebook

‘Dan majalisar mai wakiltar birnin Zariya da kewaye ya shaida cewa akwai zababbun ‘yan majalisa fiye da 200 da za su zabe shi idan an rantsar da majalisa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da Abbas ya fadawa Adeleke

"Shugabannin jam’yya (APC) sun tsaida ni a matsayin shugaban majalisar wakilan tarayya tare da Hon. Benjamin Kalu a matsayin mataimakin shugaba.
Saboda abubuwa su yi mana sauki, sai muka zo da kwamitin hadaka wanda kungiya ce mai zaman kanta kunshe da ‘yan majalisa daga jam’iyyu takwas.
Wannan kungiya mu ke so mu yi amfani da ita wajen cin ma burinmu a zaben majalisa.
Idan ka duba wakilan jam’iyyu a nan, za ka ga akwai ‘ya ‘yan jam’iyyar APC, LP, PDP da sauransu.
Ina so in tabbatar maka da cewa mun haura 200 da ke goyon bayan takara ta, an hada da ‘yan majalisa masu zarcewa da zababbu a karon farko.

Kara karanta wannan

Matakalar Taron Rantsar da Abba Gida Gida Ta Rushe Yayin Bikin Rantsar da Shi a Kano

- Hon. Tajudeen Abbas

Osun za ta bi Abbas?

An rahoto Mai girma Adeleke yana cewa za su yi biyayya ga matakin da jam’iyyar APC ta dauka a kan zaben ‘yan majalisar, kuma za su goyi bayan Abbas.

A gefe guda, Gwamnan ya na rokon a tuna da Osun, a ware masu kudin aikin filin jirgi.

SWV: Binciken Majalisa

Rahoton da mu ka fitar a baya ya ce ‘yan majalisar dattawan kasar nan sun ce Naira Tiriliyan 3 suka yi kafa a ma’aikatun tarayya tsakanin 2017 da 2021.

Binciken Sanatoci ya nuna an yi facaka da kudi a NACA, NECO, NSCDC, FERMA, da NAFDAC. Sauran inda aka tafka badakalar su ne: NEMA da DMO.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel