Sanatocin PDP Guda Biyu Sun Fice Daga Jam'iyyar a Zauren Majalisa

Sanatocin PDP Guda Biyu Sun Fice Daga Jam'iyyar a Zauren Majalisa

  • Kwanaki biyu kacal bayan rantsar da sabon shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, jam'iyyar PDP ta rasa sanatoci 2
  • Sanatocin daga jihohin Edo da Ondo sun sanar da ficewa daga PDP a zaman majalisar dattawa na ranar Laraba
  • A cewarsu, sun yanke ɗaukar wannan mataki ne saboda rigingimun cikin gida da suka dabaibaiye jam'iyyar

Abuja - Shugaban kwamitin kula da asusun gwamnati a majalisar dattawa, Sanata Matthew Urhoghide (PDP, Edo ta kudu) ya fice daga jam'iyyar PDP nan take.

Vanguard ta rahoto cewa hakan na kunshe a wata wasiƙa da Sanatan ya aike wa shugaban majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan.

Majalisa.
Ssnatocin PDP Guda Biyu Sun Fice Daga Jam'iyyar a Zauren Majalisa Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Sanatan ya ce ya ɗauki wannan mataki mai matukar wahala duba da rigingimun cikin gida wanda har yanzun aka gaza shawo kansa musamman a jiharsa ta Edo.

Haka zalika shugaban kwamitin ɗa'a, alfarma da kuma ƙorafe-ƙorafen jama'a na majalisar dattawa, Sanata Ayo Akinyelure, (PDP, Ondo ta tsakiya) ya bi sahunsa, ya fice daga PDP.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Tinubu Ya Yi Kus-Kus Da Shugaban Hukumar EFCC, Bayanai Sun Bayyana

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai dukkan Sanatocin biyu, Urhoghide da Akinyelure, ba su bayyana ƙarara cewa zasu koma jam'iyyar APC ko wata jam'iyyar siyasa ta daban ba a cikin wasikunsu.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege, wanda ya jagorancin zaman yau Laraba ne ya karanta wasikun Sanatocin guda biyu.

A ruwayar Premium Times, Sanata Urhoghide ya rubuta a wasiƙarsa cewa:

"Na rubuta wannan takarda domin sanar da majalisar dattawa a hukumance cewa na yi murabus daga kasancewa mamban jam'iyyar PDP daga yau."
"Na yanke ɗaukar wannan mataki bayan la'akari na yadda jam'iyyar ta fara rasa karsashinta sakamakon rigingimun cikin gida a matakin ƙasa kuma aka gaza shawo kansa musamman a jihata Edo."
"Yayin da wa'adin majalisa ta 9 ke dab da ƙarewa, ina taya ɗaukacin abokan aiki waɗanda zasu dawo da masu tafiya murna bisa gudummuwar da suka bayar wajen ci gaban ƙasar nan."

Kara karanta wannan

Ya Taki Sa'a: Babban Hadimin Tsohon Shugaban Kasa Buhari Ya Samu Aiki Mai Gwaɓi Bayan Karewar Mulki

Jami'an Yan Sanda Sun Mamaye Majalisar Dokokin Jihar Filato

A wani labarin na daban kun ji cewa dakarun 'yan sanda sun sake mamaye zauren majalisar dokokin jihar Filato da safiyar Laraba.

Ɗan majalisar jiha mai wakiltar mazaɓar Jos ta kudu ne ya tabbatar da haka ga manema labarai a Jos, babban birnin Filato. Ya ce zasu kira taron manema labarai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel