Sabon Gwamnan Taraba Ya Nada SSG Da Shugaban Ma’aikatansa

Sabon Gwamnan Taraba Ya Nada SSG Da Shugaban Ma’aikatansa

  • Sabon gwamnan jihar Taraba, Kefas Agbu, ya yi sabbin nade-nade yan kwanaki bayan kama aiki
  • Jemima Nathans, shugabar ma'aikatan jihar Taraba, ce ta tabbatar da ci gaban a ranar Laraba, 31 ga watan Mayu
  • A cewar Nathans, nadin babban sakataren gwamnati Timothy Kataps da shugaban ma'aikatan gwamna Jeji Williams ya fara aiki nan take

Taraba - Gwamnan jihar Taraba, Kefas Agbu ya tabbatar da nadin Timothy Kataps a matsayin sakataren gwamnatin jihar da Jeji Williams a matsayin shugaban ma'aikata.

Shugabar ma'aikatan jihar Taraba, Jemima Nathans, ce ta sanar da nade-naden a ranar Laraba, 31 ga watan Mayu, ta kuma bayyana cewa nadin ya fara aiki nan take, jaridar Punch ta rahoto.

Mukaddashin shugaban PDP da Kefas Agbu
Sabon Gwamnan Taraba Ya Nada SSG Da Shugaban Ma’aikatansa Hoto: Agbu Kefas
Asali: Facebook

Agbu Kefas ya rantsar da mutanen da ya baiwa mukamai

A halin da ake ciki, Kataps ya kasance tsohon Atoni janar kuma kwamishinan shari'a na jihar Taraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya fara rike mukamin SSG a gwamnatin marigayi Danbaba Suntai sannan ya kasance tsohonmataimakin shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na arewa maso gabas, rahoton Premium Times.

Jeji Williams ya kasance tsohon sakataren din-din-din mai ritaya. Nadin Williams ya zo a matsayin bazata ga mazauna jihar domin ana ta rade-radin Josiah Kente, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar za a ba mukamin shugaban ma'aikata.

Gwamnan Taraba ya tsige shugabannin kananan hukumomin jihar daga mukamansu

A wani labarin kuma, mun ji cewa sabon gwamnan jihar Taraba, Kefas Agbu, a ranar Talat, 30 ga watan Mayu a ya rushe shugabannin rikon kwarya na kananan hukumomi 16 da ke fadin jihar.

An tattaro a cikin wata sanarwa da kakakin watsa labarai na gwamnan, Yusuf Sanda, ya fitar cewa rushewar ta fara aiki ne daga ranar Litinin, 29 ga watan Mayun 2023.

A watan Miris din wannan shekarar ne wa'adin mulkin shugabannin ya kare amma kuma gwamnatin baya karkashin jagorancin tsohon gwamna Ishaku Dari'us ta kara musu wa'adin watanni uku.

Har ila yau, an kuma tattaro cewa sabon gwamnan ya umurce su da su mika duk wasu kayan gwamnati da ke hannunsu zuwa ga shugabannin ma'aikatan kananan hukumomin su nan ta ke.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel