Binciken Gaskiya: Tinubu Bai Sanar Da Shirin Rage Alawus Din Yan Bautar Kasa Ba

Binciken Gaskiya: Tinubu Bai Sanar Da Shirin Rage Alawus Din Yan Bautar Kasa Ba

  • Sashin binciken gaskiya ya yi watsi da rahotanni da ke yawo a dandalin Whatsapp na ikirarin cewa Shugaban kasa Bola Tinubu na shirin rage alawus din yan bautar kasa
  • Shugaba Tinubu wanda ya kama aiki a matsayin shugaban kasar damokradiyya na 5, bai yi kowace sanarwa da ke nuna rage alawus din NYSC ba
  • Wannan ikirari bai da gamsasshen hujja kuma baya kunshe a cikin jawaban da ya yi a hukumance ko a shafukan soshiyal midiya

An gano cewa hotuna da dama da masu amfani da dandalin WhatApp suka daura a shafukansu na ikirarin cewa Shugaban kasa Bola Tinubu na shirin rage alawus din da ake ba yan bautar kasa (NYSC) ba gaskiya bane.

Yan bautar kasa da Shugaban kasa Bola Tinubu
Binciken Gaskiya: Tinubu Bai Sanar Da Shirin Rage Alawus Din Yan Bautar Kasa Ba Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP, KOLA SULAIMON/AFP
Asali: Getty Images

Shugaban kasa Bola Tinubu ya fara da kafar hagu

Shugaban kasa Bola Tinubu ya kama aiki a matsayin shugaban kasar Najeriya na biyar da aka zaba bisa tafarkin damokradiyya a ranar 29 ga watan Mayu bayan nasarar da ya samu a babban zaben watan Fabrairun 2023.

Kara karanta wannan

Tinubu: Muhimman Abubuwa 7 da Aka Tsakura Daga Jawabin Sabon Shugaban Kasa

Sai dai, ya gaji kasa da ke fama da tabarbarewar tattalin arziki wanda ayyukan magajinsa, Muhammadu Buhari suka haddasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kokarinsa na daidaita lamarin, Shugaba Tinubu a cikin jawabinsa ya sanar da batun cire tallafin man fetur.

Wannan mataki da ya dauka ya haifar da tashin hankali a kasar cikin yan awanni bayan fara mulkinsa.

Sakamakon haka, ana ta rade-radin cewa ya kuma rage yawan alawus din da masu yi wa kasa hidima ke karba duk wata.

Hotuna da aka yada a dandalin WhatsApp ya yi ikirarin cewa sabon shugaban kasar ya rage alawus din yan bautar kasa daga N33,000 na gwamnatin baya zuwa N25,000.

Tinubu bai taba yin wannan jawabin ba

Dubawa ta rahoto cewa binciken kwakkwafi da aka yi kan rantsar da Tinubu ya nuna cewa bai taba yin wannan sanarwar a jawabinsa ba.

Kara karanta wannan

Tuna Baya: Dalilin da Yasa Buhari Ya Ki Yin Jawabin Rantsarwa a Shekarar 2019

Hakazalika, babu wani wuri a jawabin shugaban kasar da aka ji ya bayyana shirin rage alawus din yan bautar kasar.

Hakazalika babu wata gidar jarida da ta rahoto cewa shugaban kasar ya yi irin wannan sanarwar kuma baya kunshe a shafukansa na soshiyal midiya.

Kungiyar kwadago ta yi watsi da sabon farashin man fetur

A wani labari na daban, mun ji cewa kungiyar kwadago ta kasa ta nuna rashin amincewarta da karin farashin man fetur da kamfanin NNPC ta yi.

Kungiyar ta NLC ta ce sam wannan sabon farashi na kamfanin man kasar ba abun yarda bane inda ta nemi gwamnati da ta gaggauta bayar da umurnin janye shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel