Mataimakin Shugaban Kasa, Kashin Shettima, Ya Tabbatar da Batun Cire Tallafin Man Fetur

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashin Shettima, Ya Tabbatar da Batun Cire Tallafin Man Fetur

  • Kashim Shettima ya shiga Ofis dinsa da ke fadar shugaban ƙasa a karon farko a matsayin mataimakin shugaban ƙasa
  • Da yake zantawa da manema labarai, Shettima ya ce ya zama dole gwamnati ta kawar da tallafin man fetur
  • Ya ce masu kuɗi ne suka fi amfana da tallafin fetur yayin da talaka wa ba su san abinda ake ba sai ɗan abinda ba'a rasa ba

Abuja -Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya tabbatar da shirin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na kawo karshen tallafin man fetur a Najeriya.

Channels tv ta rahoto cewa Shettima ya dira ofishinsa da ke Villa da misalin karfe 12:39 na tsakar ranar Talata, 30 ga watan Mayu, 2023 domin fara aiki a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Kashim Shettima.
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashin Shettima, Ya Tabbatar da Batun Cire Tallafin Man Fetur Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Idan baku manta ba a jawabinsa na wurin bikin rantsarwa, Tinubu ya ayyana cewa biyan kuɗin tallafin man fetur ya zo karshe, inda ya ce kasafin 2023 bai ware kuɗin da za'a biya ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan CBN Ya Dira Aso Rock, Ya Sa Labule da Shugaba Tinubu, Bayanai Sun Fito

"Biyan kuɗin tallafin man fetur ya tafi," Tinubu ya bayyana a Eagle Square ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, 2023 bayan ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban ƙasa na 16.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shettima ya tabbatar da lamarin

Da yake jawabi ga manema labaran gidan gwamnati, Mataimakin shugaban ƙasa ya jaddada kalaman uban gidansa kan batun cire tallafin man fetur.

Ya ce sabon shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shirya inganta rayuwar talakan Najeriya a zangon mulkinsa na tsawon shekaru huɗu.

Daily Trust ta rahoto Shettima na cewa:

"Shugaban ƙasa ya riga ya yi jawabi game da batun tallafin man fetur jiya. Maganar gaskiya ita ce ko dai mu kawar da tallafin ko kuma shi ya ga bayan Najeriya a matsayin ƙasa."
"A 2022, mun kashe $10bn wajen tallafin da zai ƙara inganta salon rayuwar masu kuɗi saboda ni da kai ne muke amfana da kaso 90% na tallafin, sauran talakawa kuwa kaɗan su ke amfana."

Kara karanta wannan

Fetur Ya Haura N300 a Gidajen Mai Daga Jin Bola Tinubu Ya Sanar da Janye Tallafi

Gwamna Kwara Ga Yan Kasuwa: Duk Wanda Ya Boye Fetur Zan Kwace Lasisinsa

A wani rahoton kuma Gwamnan Kwara ya sha alwashin kwace shaidar mallaka na duk gidan man da aka kama yana wahal da yan jiharsa.

AbdulRazak ya ce gwamnati ta biya tallafin Fetur ɗin da suka tara, don haka ba dalilin da zai sa yan kasuwa su ƙuntatawa talakawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel