"Na Shirya Zuwan EFCC," Gwamna Samuel Ortom Ya Yi Magana Kan Bincike

"Na Shirya Zuwan EFCC," Gwamna Samuel Ortom Ya Yi Magana Kan Bincike

  • Gwamna Ortom na jihar Benuwai ya ce ya shirya tsaf domin amsa gayyatar hukumar EFCC bayan ya bar mulki
  • Ortom, mamban jam'iyyar PDP ya ce shi ba matsoraci bane da zai tattara ya bar ƙasar nan domin gujewa kamen EFCC
  • Haka nan ya ce ba zai rushe majalisar zartarwansa ba har zuwa ranar miƙa mulki 29 ga watan Mayu, 2023

Benue - Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya ce baya tsoron hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) kuma zai miƙa kansa idan ta kira shi.

Gwmana Ortom ya ce a shirye yake hukumar ta bincike shi saboda ba shi ba wani shafaffe da mai bane kuma babu wani abu da yake ɓoye wa, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Canja Fasalin Naira: An Faɗi Matakan da Ya Kamata Tinubu Ya Ɗauka Kan Gwamnan CBN da Wasu Jiga-Jigai

Gwamna Ortom.
"Na Shirya Zuwan EFCC," Gwamna Samuel Ortom Ya Yi Magana Kan Bincike Hoto: Samuel Ortom
Asali: UGC

Ortom ya bayyana haka ne ranar Jumu'a a wurin taron bankwana da mambobin majalisar zartaswa da sauran kusoshin gwamnati wanda ya gudana a gidan gwmanatin Benuwai, Makurɗi.

Gwamnan ya shawarci waɗanda suka rike muƙamai a gwamnatinsa

Haka nan kuma gwamna Ortom ya shawarci dukkan waɗanda ya naɗa a gwamnatinsa su shirya tunkarar hukumar EFCC idan ta gayyace su domin amsa tambayoyi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa ya ce:

"A duk lokacin da EFCC ta gayyace ku, kar gabanku ya faɗi, ku miƙa musu kanku. Ni ba matsoraci bane da zan gudu sabida EFCC ba, idan suka zo wurina, da kafata zan bi su."
"Bani da wasu hannayen jari a nahiyar turai, a nan jihar Benuwai na zuba hannun jari na. Idan wani ya tuhume ni da aikata laifi, to a ba shi dama ya nuna yadda abun ya faru saboda bana tsoron kowa."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Kori Kwamishinoni da Hadimai, Ya Kafa Musu Sharaɗi

Shin ya sallami dukkan naɗe-naɗensa daga aiki?

Ortom ya kara da cewa ba zai rushe majalisar zartarwansa ba kana ya umarci Kwamishinoni su koma Ofis su ci gaba da ayyukansu har zuwa ranar miƙa mulki.

A ruwayar Tribune, gwamnan ya ƙara da cewa:

"Daga yau har zuwa ranar 29 ga watan Mayu, 2023 lokacin da sabuwar gwamnati mai jiran gado zata kama aiki kunan nan kan muƙamanku, sai lokacin zaku bar Ofis."

Gwamnan Inuwa Yahaya Ya Sallami Mambobin Majalisar Zartarwan Gombe

A wani labarin kuma Shugaban gwamnonin arewa ya kori kwamishinoni da hadimai, ya Kafa musu sharaɗi.

Gwamnan Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya rushe majalisar zartarwan jiharsa, amma ya ce su zauna a Ofis zuwa ranar ƙarshe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel