Reno Omokri Ya Bayyana Wadanda Tinubu Zai Ba Wa Mukamai A Gwamnatinsa

Reno Omokri Ya Bayyana Wadanda Tinubu Zai Ba Wa Mukamai A Gwamnatinsa

  • Tsohon mai ba da shawara ga Goodluck Jonathan ya yi hasashen cewa magoya bayan Peter Obi za su samu mukamai a gwamnatin Tinubu
  • Omokri wanda ya goyi bayan dan takarar PDP a zaben da ya gabata ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a ranar Laraba 25 ga watan Mayu
  • Omokri ya kasance mai ba da shawara a lokacin mulkin tsohon shugaba Jonathan, kuma magoyin bayan jam’iyyar adawa ta PDP a kasar

Abuja - Tsohon mai ba da shawara ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Remo Omokri ya yi hasashen cewa magoya bayan Peter Obi za su iya fitowa a jerin masu mukamai a gwamnatin Bola Tinubu.

Omokri ya bayyana haka ne a kafar sada zumunta inda ya ce ‘Obidients’ an yi amfani da su kuma an watsar da su, cewar Legit.ng.

Omokri/Tinubu
Peter Obi: Reno Omokri Ya Yi Hasashen Wadanda Za a Ba Wa Mukamai. Hoto: Reno Omokri, Bola Tinubu.
Asali: Twitter

‘Obidient’ na nufin magoya bayan Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, na gaskiya

Omokri ya rubuta a shafinsa kamar haka:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ku bari sai Tinubu ya sanar da gwamantinsa, idan har kotun koli ba ta bayyana takararsa a matsayin wadda ba ta inganta ba kamar yadda muke addu’a.
“Zaku ga manyan magoya bayan Peter Obi har ‘yan kafar sada zumunta a gwamnatin Tinubu suna rubutu akansa.
“A lokacin ne zaku san anyi amfani daku an watsar daku kamar kunzugu da ya gama aikinsa.”

Omokri ya kasance mai goyon bayan PDP

A lokacin zabe, Omokri ya goyi bayan dan takarar PDP, Atiku Abubakar, wanda yazo na biyu a zaben, duk tsawon wannan lokaci Omokri ya na ta fadi in fada da magoya bayan Peter Obi.

Mutane da dama sun mayar masa da zafafan martani

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu a daidai lokacin da ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda suka zarge shi da mai yada barna.

Colif Isabor:

“Reno, wannan barna kake aikata wa anan, an san Tinubu da yafiya har wadanda suka kasance manyan abokan gabansa, kuma shine ake ganin zai hada kan ‘yan Najeriya, ba abin mamaki bane ya dauko dan adawa ya bashi matsayi.

Benu Joseph:

“Baka san su waye asalin magoya bayan Peter Obi ba, kamanta da wadanda suke nuna kansu, Obidients sun fi karfin neman matsayi, damuwarmu mu kawo sauyi a kasa da tabbatar da dimukradiya da kuma saka matasa a harkokin siyasa.

Enyiaku Victor:

"@renoomokri, kawai ka fada mana kanason sauya sheka zuwa APC...Ba wanda zai doke ka.”

Tinubu Ya Yi Amfani da Obi, Ya Hana Atiku Samun Mulki, Dan Takaran LP

A wani labarin, wani dan takarar gwamna a jihar Oyo a jam'iyyar Labour, Tawfiq Akinwale ya bayyana yadda Tinubu ya yi amfani da Peter Obi.

Tawfiq ya ce Asiwaju Bola Tinubu ya roki Pat Utomi ya dakatar da takararsa don cimma burinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel