Yadda Tinubu Ya Yi Amfani da Obi, Ya Hana Atiku Samun Mulki Inji ‘Dan Takaran LP

Yadda Tinubu Ya Yi Amfani da Obi, Ya Hana Atiku Samun Mulki Inji ‘Dan Takaran LP

  • Tawfiq Akinwale ya fito yana ikirarin Bola Ahmed Tinubu ya roki Pat Utomi ya janye takararsa
  • Farfesan ya samu tikitin Jam’iyyar LP, amma ya sallama takararsa ga Peter Obi da ya zo na uku a 2023
  • ‘Dan takaran LP a zaben Gwamnan Oyo ya ce Tinubu ya taimakawa takarar Obi a Jam’iyyar adawar

Ibadan, Oyo - Tawfiq Akinwale wanda ya yi wa jam’iyyar LP takarar Gwamna a jihar Oyo ya bayyana abin da ya faru a zaben 2023 ta bayan fage.

Da aka yi hira da shi a gidan rediyon YES FM a garin Ibadan, Tawfiq Akinwale ya ce Asiwaji Bola Tinubu ne ya roki Pat Utomi ya hakura da takara.

Zababben shugaban kasar ya shawo kan Farfesa Utomi, ya bar Peter Obi ya nemi kujerar shugaban kasa a madadinsa a jam’iyyar LP mai adawa.

Kara karanta wannan

Zaman da Kwankwaso Ya Yi da Tinubu a Faransa Zai Iya Canza Siyasar APC da Majalisa

Tinubu
Obi, Tinubu, Atiku, Utomi Hoto: KOLA SULAIMON/AFP, PIUS UTOMI EKPEI/AFP
Asali: Getty Images

‘Dan takaran Gwamnan yake cewa har Utomi ya samu takarar shugaban kasa, amma da Tinubu ya lallabe shi, sai ya kyale Obi ya rike tutar jam’iyyar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Akinwale ya ce Tinubu ya kware sosai a siyasa, rokon Utomi da ya yi ya hakura da neman takara a 2023 ya jawo Peter Obi ya yi wa jam’iyyar PDP illa.

An hana Atiku kai labari

An rahoto jigon na LP ya na mai cewa zababben shugaban kasar ya yi haka ne saboda ya toshe damar da Atiku Abubakar yake da ita na yin nasara.

A jawabin da ya yi da Yarbanci a gidan rediyon, ‘dan siyasar ya bayyana tsohon Gwamnan na Anambra da yaron Tinubu, ya ce da shi APC tayi amfani.

Haka zalika ‘dan siyasar ya yi ikirarin cewa kudin da Tinubu ya ba Utomi ne aka yi amfani da su wajen tallata Obi wanda a karshe ya ba kowa mamaki.

Kara karanta wannan

Minista Ya Cigaba da Korar Shugabannin Hukumomi, Ya Ce Babu Sani ko Sabo a Mulki

Mista Akinwale ya ce Tinubu bai yi tunani ‘dan takaran na LP zai iya irin farin jinin da ya yi a zaben na bana ba, ya samu kuri'u fiye da miliyan shida.

Obi ya samu tikiti a sama

Bayan ‘dan takaran mataimakin shugaban kasan 2019 ya bar PDP ne Utomi, Faduri Joseph da Olubusola Emmanuel-Tella su ka janye masa takararsu.

‘Dan siyasar ya samu tutar LP ba tare da hamayya ba, a karshe ya hana jam’iyyar adawa ta PDP samun kuri’u a Kudu maso kudu da kudu maso gabas.

Zaben jihar Kano

Labari ya zo cewa a yau za a fara sauraron shari’ar Abdulsalam Abdulkarim Zaura da hukumar INEC, jam’iyyar NNPP da Rufai Hanga a kotun karar zabe.

NNPP ta samu kujerun Majalisar Dattawa biyu a 2023, ‘Dan takaran na APC watau AA Zaura ya na so ya karbe daya, a cewarsa magudi aka yi aka doke shi.

Kara karanta wannan

Muhimman Abu 2 da Suka Jawo Allah Ya Hana Atiku da Peter Obi Mulkin Najeriya a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel