Majalisa Ta 10: Yadda ’Yan Majalisu Ke Raba Daloli Don Neman Goyon Bayan a Zabe Su

Majalisa Ta 10: Yadda ’Yan Majalisu Ke Raba Daloli Don Neman Goyon Bayan a Zabe Su

  • Ana zargin ‘yan takarar shugabancin majalisun tarayya da raba daloli don samun goyon bayan ‘yan uwansu a majalisar ta 10
  • Wannan na zuwa ne makwanni uku kafin kaddamar da majalisar ta 10 a watan Yuni mai kamawa
  • Sanata Ali Ndume na jihar Borno a wata hira da ya yi da BBC Hausa ya tabbatar da Sanatocin na raba daloli

Abuja – Yayin da ake gab da kaddamar da majalisa ta 10 a watan Yuni, masu neman kujerar majalisar da dama sun fara raba daloli don neman goyon bayan ‘yan uwansu a majalisar.

Daga cikin manya-manyan masu neman wannan kujera akwai Godswill Akpabio (Akwa Ibom), Abdulaziz Yari (Zamfara) da kuma Orji Uzor Kalu (Abia).

Tinubu/yan majalisa
Majalisa Ta 10: Bincike ya Nuna Yadda ’Yan Majalisu Ke Raba Daloli Don Neman Goyon Baya. Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar Legit ta tattaro cewa, ana zargin masu neman takarar kujerar da cire makudan kudade na daloli don ganin ‘yan majalisar sun zabe su a yayin kaddamar da majalisar ta 10.

Kara karanta wannan

Kungiyar MURIC Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Kirista Dan Kudu a Shugabancin Majalisar Dattawa

Jerin 'yan majalisun da ke son kujarar majalisar wakilai

Yayin da a majalisar wakilai kuma, daga cikin manya-manyan ‘yan takarar kujerar akwai Tajudden Abbas (Kaduna) da Yusuf Gagdi (Plateau) da Aminu Sani Jaji (Zamfara).

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sauran sun hada da mataimakin shugaban majalisar Ahmed Idris Wase (Plateau) da Mukhtar Betara (Borno) da Mariam Odinaka (Imo) da sauransu.

Majiyoyi sun tabbatar cewa takarar ta koma ta wanda ya fi kowa ba da kudi, yayin da ake ta gasar raba kudade duk da umarnin jam’iyyar na zaban wadanda suke so su gaji kujerun.

Sanata Ali Ndume na Borno ya magantu

A wata hira da BBC Hausa, Sanata Ali Ndume (APC, Borno) ya bayyana yadda ‘yan majalisun ke raba daloli don ganin sun shawo kan ‘yan majalisar.

A cewarsa:

“Akwai wasu Sanatoci da ke son kujerar suna ba da makudan kudade don samun kuri’u.

Kara karanta wannan

Doguwa, ‘Yan APC 2 Sun Hakura da Kujerar Majalisa, Sun Ayyana ‘Dan Takararsu

“Wasu Sanatocin sun tabbabar cewa duk da umarnin jam’iyyar amma ba su bar raba daloli ba kuma sun nuna ba za su janye wannan muradi nasu na tsayawa takara ba.”

Majalisa Ta 10: Tinubu Ya Bayyana Zabin Sa a Shugabancin Majalisar Dattawa

A wani labarin, zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana Godswill Akpabio a matsayin wanda zai gaji kujerar majalisar dattawa.

Yayin da Sanata Barau Jibrin zai kasance mataimakinsa a majalisar da ake sa ran kaddamar da ita a watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel