Doguwa, ‘Yan APC 2 Sun Hakura da Kujerar Majalisa, Sun Ayyana ‘Dan Takararsu

Doguwa, ‘Yan APC 2 Sun Hakura da Kujerar Majalisa, Sun Ayyana ‘Dan Takararsu

  • Takarar Majalisa ta canza domin Alhassan Ado Doguwa ya koma goyon bayan Hon. Tajuddeen Abbas
  • ‘Dan majalisar na Tudun Wada da Doguwa ya halarci taro inda aka ga Abbas da Hon. Benjamin Kalu
  • Hon. Doguwa ya tabbatar da cewa ya fasa neman takara a majalisa tun da APC ta raba masu gardama

Abuja - Alhassan Ado Doguwa wanda shi ne shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan tarayya, ya hakura da kujerar da yake burin samu a majalisa.

Rahoton da aka samu daga The Cable, ya tabbatar da cewa a halin yanzu Honarabul Alhassan Ado Doguwa bai cikin masu takarar shugabancin majalisa.

Alhassan Ado Doguwa ya sanar da hakan ne a ranar Laraba da daddare lokacin da ya gana da wasu zababbun ‘yan majalisar tarayya a wani otel a Abuja.

Kara karanta wannan

Bayanai Sun Cigaba da Fitowa Kan Mutanen da Tinubu Zai Ba Mukamai a Gwamnati

Doguwa
Hon. Alhassan Ado Doguwa a Aso Rock Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da ‘yan takaran da APC ta tsaida, Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu sun halarci zaman da aka yi jiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ware kujeru ya cire Maki da Olawuyi

Rahoton ya ce Hon. Abubakar Maki da Hon. Olatunji Olawuyi duk sun hakura da takararsa da suka yi niyya a zaben shugabanni majalisa ta goma.

Doguwa ya ce Hon. Abbas mai wakiltar mazabar Zaria ya cancancanta ya jagoranci ragamar mutane 359 da za a rantsar a majalisar wakilan Najeriya.

Hakan ya na zuwa ne bayan an yi tunanin shugaban masu rinjayen ya na cikin masu yakar Abbas, ya na goyon bayan 'yan kungiyar G7 da ke majalisa.

An ragewa 'Yan G7 karfi

‘Dan majalisar na Tudun Wada da Doguwa yake cewa ya hakura da takararsa ne a ranar da jam’iyyar APC ta ayyana Tajuddeen Abbas da Ben Kalu.

Kara karanta wannan

‘Yan PDP, LP da NNPP Fiye da 100 Su Na Goyon Bayan ‘Dan Takaran APC a Majalisa

Kamar yadda PM News ta fitar da labari a daren yau, Doguwa wanda ya dade a majalisa ya nuna zai goyi bayan Tajudeen Abbas ya gaji Gbajabiamila.

“Ka da ayi tunanin tsautsayi ya kawo ni nan. Masu tunanin mafarki su ke yi, ba mafarki ba ne wannan. Wannan shi ne zahiri.”

- Alhassan Ado Doguwa

Wannan lamari zai taimakawa jam’iyyar APC da ‘yan takaranta a zaben da za ayi a Yuni.

Abbas/Kalu sun samu karbuwa

A baya an samu rahoto cewa takarar Hon. Tajuddeen Abbas da Hon. Benjamin Kalu ta na cigaba da samun goyon baya a Majalisa a kan gungun 'Yan G7.

Wasu Gwamnonin jihohi da kuma ‘yan PDP, LP, SDP, NNPP da sauran jam’iyyun adawa za su marawa Tajuddeen Abbas baya ya zama shugaban majalisa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel