Gwamna Ganduje Ya Yi Wa Mutanen Kano Alkawarin Cewa Jam'iyyar APC Za Ta Dawo a Jihar

Gwamna Ganduje Ya Yi Wa Mutanen Kano Alkawarin Cewa Jam'iyyar APC Za Ta Dawo a Jihar

  • Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya sha alwashin cewa jam'iyyar APC za ta sake farfaɗowa a jihar
  • Gwamna Ganduje ya ce jam'iyyar za ta bar madafun ikon jihar ne kawai na wanu ɗan gajeran lokaci kafin ta sake dawowa
  • Ganduje ya ce tarihi zai maimaita kansa na abinda aka taɓa yi wa tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano mai barin gado, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa jam'iyyarsa ta All Progressive Congress (APC), za ta bar jihar Kano ne kawai na wani ɗan lokaci, kafin ta sake dawowa.

Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa Ganduje, ya yi wannan furucin ne wajen ƙaddamar da sabuwar hanyar da aka yi a Kwanar Dala, cikin ƙaramar hukumar Dala ta jihar, a yammacin ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Sabuwar Rigima Ta Ɓalle a Jam'iyyar APC Kan Zaben Shugaban Kasa, Bayanai Sun Fito

Gwamna Ganduje ya ce APC za ta sake dawowa a Kano
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Gwamna Ganduje ya kuma nemi yafiyar al'ummar jihar waɗanda ya ɓatawa rai a lokacin da ya kwashe kan madafun ikon jihar, cewar rahoton The Guardian.

A kalamansa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Wannan hanyar aikinta ya kammala sannan gashi yanzu mun taro anan domin ƙaddamar da ita. Wannan ƙaɗɗamarwar mun yi mata laƙabin ta bankwana, saboda tana ɗaya daga cikin ayyukan ƙarshe da za mu ƙaddamar domin yi wa al'ummar Kano bankwana, amma na ɗan gajeran lokaci."

Dawo-dawo: Tarihi zai maimaita kansa

Ganduje ya ce tarihi zai maimaita kansa dangane da Dawo-Dawo, (shahararriyar waƙar da aka yi wa sanata Rabiu Musa Kwankwaso domin ya dawo ya sake mulkar jihar, bayan mulkinsa na farko).

A cewarsa:

"Ko Dawo-Dawo da aka yi a baya, mu ne mu ka tsaya tsayin daka ta tabbata, saboda haka yanzu kada mu manta da waƙar dawo-dawo."

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Taraba Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Batun Fitar Da N2bn a Asusun Jihar Domin Siyo Motocin Kece Raini

Ganduje ya kuma ƙaddamar da wasu hanyoyin guda uku da suka haɗa da hanyar Bello Kano, hanyar Kwanar Dala da wata kuma a Babban Layi Kurnar Asabe, cikin ƙaramar hukumar Dala ta jihar.

Wallahi Ko a 2019, Abba Gida Gida Ya Ci Zaben Gwamnan Kano - 'Yar APC Ta Fasa Kwai

A wani rahoton na daban kuma, wata jigo a jam'iyyar APC a jihar Kano ta fasa kwai kan sahihin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar, a zaɓen 2019.

Hajiya No Shaking ta bayyana cewa duk da ita ƴar jam'iyyar APC ce, tabbas Abba Gida-Gida ne ya lashe zaɓen gwamnan jihar a shekarar 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel